Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da yaki da laifuka a intanet, domin magance yaduwar labaran bogi wanda zai iya kawo rudani a zukatan mutane.
Babban hafsan sojojin kasan Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya sanar da hakan a wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Janar Buratai ya ce sabon sashen zai taimaka wajen yaki da al'amuran da suka shafi ta'addanci a intanet.
Ya kuma ce sojojin za su kaddamar da wata manhajar waya don taimakawa mutane wajen kai karar sojoji masu cin zarafin mutane.
Mutane za su iya sanya bidiyo a kan manhajar wayar don kafa hujja game da korafe korafensu, wanda za su iya dorawa ba tare da an san ko waye ya dora ba.
No comments:
Write blogger