Ana kara matsa wa Saudiyya lamba kan ta yi cikakken bayani kan makomar dan jaridar nan Jamal Khashoggi, a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ke gana wa da sarki Salman a birnin Riyadh.
An yi wa Khasoggi ganin karshe a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santabul na Turkiya mako biyu da suka gabata.
Hukumomin Turkiya na da yakinin cewa jami'an Saudiyya ne suka kashe dan jaridar, sai dai hukumomin Saudiyya sun musanta zargin.
Sai dai kafofofin watsa labaran Amurka na cewa, da alama Saudiyya na shirin tabbatar da cewa Khashoggi ya mutu a lokacin da aka samu matsala yayin da ake yi masa tambayoyi.
A dare daya, rundunar 'yan sandan Turkiyya ta gama binciken ofishin jakadancin bayan da hukumomin Saudiyya su ka ba su damar shiga.
- Jamal Khashoggi: Amurka da Burtaniya na iya kauracewa taron Saudiyya
- 'Turkiyya na da shaida a kan kisan Khashoggi'
- Wane ne Jamal Khashoggi? Dan jaridar Saudiyyan da ya yi batan dabo
Me zai fito daga tattaunawar Sarki Salman da Pompeo?
Sakataren harkokin wajen da sarkin sun gana a Riyadh.
Yayin da ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Mista Pompeo ya yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga Sarki Salman kan "jajircewarsa, da binciken gaskiya" a kan bacewar Mr Khashoggi.
Ana kuma sa rai Mr Pompeo zai nemi karin bayani kan wata hira tsakanin sarkin da Shugaba Donald Trump ranar Litinin.
Mr Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter cewa: "Yanzu na gama magana da Sarkin Saudiyya, wanda ya ce ba shi da masaniya kan abin da ya faru ga dan kasarsa."
Daga baya kuma, Trump ya shaida wa 'yan jarida cewar: "Ya musanta da kakkausar murya. A ganina, watakila 'yan bindiga ne suka kashe shi. Wa ya sani?"
Akwai abubuwa da dama tattare da wannan lamarin, ganin cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin Saudiyya da Amurka.
Mr. Trump dai ya riga ya bayyana cewa ba zai soke wata yarjejeniyar makamai mai tsoka ba tsakanin kasarsa da Saudiyya.
Amma ya yi barazanar yin hukunci mai tsauri idan aka gano masarautar da hannu a kashe Khashogi.
Sarki Salman ya bayar da umarnin yin bincike kan batan dan jaridar ranar Litinin.
Sai dai a jerin sanarwar da Saudiya ta fitar kawo yanzu, sun yi watsi da zargin da ake yi wa kasar kan kisan.
A na sa rai Mr Pompeo zai gana da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a Riyadh.
Daga nan kuma sakataren harkokin wajen zai je Turkiyya.
Me ya faru a binciken ofishin jakadancin?
A karon farko tun bacewar dan jaridar ran 2 ga watan Oktoba, an kyale masu bincike a Turkiyya su shiga cikin ginin.
Tawagar Saudiyya ce ta fara shiga ranar Litinin, sai tawagar 'yan sandan binciken Turkiyya ta shiga.
An ruwaito cewar sun dauki samfurin kasar lambun ofishin jakadancin.
Abun da ake zargin ya faru a Satambul
Gani na karshe da aka yi wa Mr Khashoggi, mai sukar gwamnatin Saudiyya a rubuce-rubucensa, ranar 2 ga watan Oktoba ne yayin da yake shiga ofishin jakadancin.
Rahotanni sun nuna cewa an far wa Khashoggi a ofishin bayan da ya shiga ya karbo takardun aurensa.
Majiyoyi a Turkiyya na ganin cewa wata tawagar karfafan mutane 15 masu kisa 'yan Saudiyya ce ta kashe shi, amma Saudiyyar ta dage a kan cewar ya fita daga ofishin cikin koshin lafiya.
A baya dai, Mr Khashoggi mai bai wa masarautar Saudiyya shawara ne kafin dangantakarsu ta yi tsami, inda daga baya ya yi gudun hijira na rajin kai.
No comments:
Write blogger