spon

Showing posts with label labaran duniya. Show all posts
Showing posts with label labaran duniya. Show all posts

Monday, November 26, 2018

Sojojin sama sun tarwatsa wasu rundunonin Boko haram,bayen harin da aka kaiwa sojojin Nigeria a metele

Rundunar sojojin sama suntashi rundunar Boko haram bayan harin da akakaiwa rundunar sojojin Nigeria a (Metela) a barno
*adadin sojojin da akakashe yakai misalin 130 hakan neyasa yarazana rundunar sojojin kasar Nigeria
*Wannan harin yabigi kowa tundaga kan gwamnatin harzuwa al,umar kasannan

Thursday, November 1, 2018

ZAZZAFA:WAKAR GWANNA BARAWO MAI WAKA BARAWO

*wakar da akafitar zazzafa ta gwamna barawo mai waka barawo

GANDUJE VS JAFAR JAFAR

Thursday, October 18, 2018

TABBAS DAUKE WUTAR LANTARKI YANA GAB DA ZAMA TARIHI A KASARNAN

Kamar yadda boko Haram take dab da zama tarihi a Kasarnan....

Haka kuma rashin tsaro sai dai mu ba na bayanmu labarin cewar a baya anyi rashin tsaro....

Haka kuma fita waje don sawo kaya na tabbatar diyana da zan haifa nan gaba in sha Allah ba zasu fita waje don sawo kaya ba domin muna dab da kera komai made in Nigeria da yardar Allah.....

Haka kuma cin hanci a Kasarnan yana dab da zama tarihi......

Uwa Uba kuma Rashin aikinyi in Allah ya yarda nan gaba sai Kowa ya zabi irin aikin da yake son yi.......

Da yardar Allah sai Nigeria ta shiga cikin kasashe  mafi daraja a doron kasa..

Ya Allah ka taimaki Baba Buhari akan aniyarsa ta gyaran kasa

Wednesday, October 17, 2018

HABAICIN ATIKU GA BUHARI: ‘Ni ba zan shafe wata shida ban nada ministoci ba

                                      ATIKU VS BUHARI

Ali Artwork Yayi Raddi Ka Jaruman Da Suke Kare Ganduje

Shahararren Dan Comedy nan  kuma mai editing  na bidiyo na kannywood Ali Muhammad Idris wanda akafi sani da (Ali Artwork) ya kasance kwararen mai editi wanda kusan duk shekara shine yake zama gwarzon Shekara a bangaren masu editing, wanda kusan ya samu lambar yabo wato (Award) daga kungiyoyi da kamfanoni da dama.

Ya samu lambar yabo a wajan ministan gada labarai Lai Muhammad shine ya Bashi Kyautar warzon Ahekara A 2016,  ‘yan kwanakinnan ma anyi bikin karramashi tare da bashi lambar yabo a lagos.

Jarumin ya kware a fanin editing na bidiyo yana iya maida hoto mara motsi ya kuma yana motsi.

Dan haka jarumk Ali Artwork ya dabbatar da bidiyon Da Jafar Jafar ya saki na gwamnan kano wanda akace hawa akai, ali artwork yace bidiyon na gaske ne ba wai hadi.
Kuma yayi kira ga jaruman fim wadanda suke kokarin kare gwamna ganduje da su daina wahalar da kansu.

Dadin dadawa jarumin ya kara da cewa wai ba dan shi ya kasance magoyin bayan tsohon gwamna kwankwaso bane yace haka,

Kudai kalli bidiyon kuje cikake labarin daga bakinsa

Tuesday, October 16, 2018

Saudiyya na fusantar matsin lamba kan batan Jamal Khashoggi

Mr Pompeo ya gode wa Sarki Salman saboda jajircewa kan binciken
Ana kara matsa wa Saudiyya lamba kan ta yi cikakken bayani kan makomar dan jaridar nan Jamal Khashoggi, a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ke gana wa da sarki Salman a birnin Riyadh.
An yi wa Khasoggi ganin karshe a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santabul na Turkiya mako biyu da suka gabata.
Hukumomin Turkiya na da yakinin cewa jami'an Saudiyya ne suka kashe dan jaridar, sai dai hukumomin Saudiyya sun musanta zargin.
Sai dai kafofofin watsa labaran Amurka na cewa, da alama Saudiyya na shirin tabbatar da cewa Khashoggi ya mutu a lokacin da aka samu matsala yayin da ake yi masa tambayoyi.
A dare daya, rundunar 'yan sandan Turkiyya ta gama binciken ofishin jakadancin bayan da hukumomin Saudiyya su ka ba su damar shiga.

Me zai fito daga tattaunawar Sarki Salman da Pompeo?

Sakataren harkokin wajen da sarkin sun gana a Riyadh.
Yayin da ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Mista Pompeo ya yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga Sarki Salman kan "jajircewarsa, da binciken gaskiya" a kan bacewar Mr Khashoggi.
Ana kuma sa rai Mr Pompeo zai nemi karin bayani kan wata hira tsakanin sarkin da Shugaba Donald Trump ranar Litinin.
Mr Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter cewa: "Yanzu na gama magana da Sarkin Saudiyya, wanda ya ce ba shi da masaniya kan abin da ya faru ga dan kasarsa."
Daga baya kuma, Trump ya shaida wa 'yan jarida cewar: "Ya musanta da kakkausar murya. A ganina, watakila 'yan bindiga ne suka kashe shi. Wa ya sani?"
Akwai abubuwa da dama tattare da wannan lamarin, ganin cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin Saudiyya da Amurka.
Mr. Trump dai ya riga ya bayyana cewa ba zai soke wata yarjejeniyar makamai mai tsoka ba tsakanin kasarsa da Saudiyya.
Amma ya yi barazanar yin hukunci mai tsauri idan aka gano masarautar da hannu a kashe Khashogi.
Sarki Salman ya bayar da umarnin yin bincike kan batan dan jaridar ranar Litinin.
Sai dai a jerin sanarwar da Saudiya ta fitar kawo yanzu, sun yi watsi da zargin da ake yi wa kasar kan kisan.
A na sa rai Mr Pompeo zai gana da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a Riyadh.
Daga nan kuma sakataren harkokin wajen zai je Turkiyya.
Presentational grey line

Me ya faru a binciken ofishin jakadancin?

A karon farko tun bacewar dan jaridar ran 2 ga watan Oktoba, an kyale masu bincike a Turkiyya su shiga cikin ginin.
'Yan sandan Turkiyya sun yi bincike a ofishin jakadancin Saudiyya a SantambulHakkin mallakar hotoEPA
Image caption'Yan sandan Turkiyya sun yi bincike a ofishin jakadancin Saudiyya a Santambul
Tawagar Saudiyya ce ta fara shiga ranar Litinin, sai tawagar 'yan sandan binciken Turkiyya ta shiga.
An ruwaito cewar sun dauki samfurin kasar lambun ofishin jakadancin.

Abun da ake zargin ya faru a Satambul

Hotunan kyamarorin tsaro na CCTV sun nuna dan jaridar dan kasar Saudiyya yana shiga karamin ofihin jakadancin Saudiyya a birnin Santanbul na Turkiyya.
Gani na karshe da aka yi wa Mr Khashoggi, mai sukar gwamnatin Saudiyya a rubuce-rubucensa, ranar 2 ga watan Oktoba ne yayin da yake shiga ofishin jakadancin.
Rahotanni sun nuna cewa an far wa Khashoggi a ofishin bayan da ya shiga ya karbo takardun aurensa.
Majiyoyi a Turkiyya na ganin cewa wata tawagar karfafan mutane 15 masu kisa 'yan Saudiyya ce ta kashe shi, amma Saudiyyar ta dage a kan cewar ya fita daga ofishin cikin koshin lafiya.
A baya dai, Mr Khashoggi mai bai wa masarautar Saudiyya shawara ne kafin dangantakarsu ta yi tsami, inda daga baya ya yi gudun hijira na rajin kai.