Sunday, June 10, 2018
[Music] Rarara -Fulogan Wasu Sunsha Mai Sai Nishi
Sabuwar wakar Dauda Kahuhu Rarara Da Yayiwa Shugaban Kasa Baba Buhari Mai Suna Sai Kayi TAwakar GMB Fulgan Wasu Sunsha Mai Sai NIshi.
Yayin da wasu ke kin shugaba buhari wasu kuma sansa suke da.
DOWNLOAD MUSIC HERE
Yayin da wasu ke kin shugaba buhari wasu kuma sansa suke da.
DOWNLOAD MUSIC HERE
Saturday, June 9, 2018
[Music] Aminu -Rarara Yaci Kudin Mawaka
Sabuwar wakar da akayiwa rarara wace yaci kudin mawakan APC Naira ” Miliyan Dari ” yadda mawakin yace.
To kawai ku saurari wakar domin kuji mai tazo dashi.
Tuesday, June 5, 2018
Yaran comedy: Buhariyya Episode 2
Yaran comedy Episode 2
wata rana ana zaunane gari yaci wuta ba kudi sai suka gano wata bakalleda sukatafi da gudu ana rigerige suna zuwa aka Fara tureture sai ogansu sai shima yatawo yana zuwa yadauki bakalleda yana budewa kun san mai yagani sai kunkalla zaku sha dariyya
wata rana ana zaunane gari yaci wuta ba kudi sai suka gano wata bakalleda sukatafi da gudu ana rigerige suna zuwa aka Fara tureture sai ogansu sai shima yatawo yana zuwa yadauki bakalleda yana budewa kun san mai yagani sai kunkalla zaku sha dariyya
Majalisun Nijeriya Sun Gindaya Wa Shugaba Buhari Wasu Dokoki Guda 12
Majalisun Nijeriya Sun Gindaya Wa Shugaba Buhari Wasu Dokoki Guda 12
...idan bai bi ba za mu dauki mataki, cewar majalisun
Majalisun dokokin Nijeriya sun amince da wasu kudurori 12 da suka ce wajibi ne gwamnatin Muhamadu Buhari ta aiwatar da su ko kuma su dauki mataki.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya karanta matsayar da suka cima bayan wani zama na musamman da suka yi domin duba halin da kasar take ciki, wanda wasunsu suka ce yana ci gaba da tabarbarewa.
Ya ce majalisun biyu sun amince cewa wajibi ne Shugaba Buhari ya dauki alhakin abubuwan da mutanen da ya nada suke yi, sannan ya dauki mataki kan duk wanda ya saba wa doka da yin barazana ga demokuradiyya.
Suka kara da cewa wajibi ne jami'an tsaro su tunkari kashe-kashen da ake yi a kasar, sannan a daina takura wadanda ake wa kallon 'yan adawa ne ko kuma masu bambancin ra'ayi da bangaren zartarwa.
"Majalisa ba za ta yi wata-wata ba wurin daukar mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu domin aiwatar da wadannan kudurori da aka a mince da su yau (Talata)".
Wannan zama na zuwa ne a lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shugabannin majalisar.
Kudurori 12
*Kawo karshen kashe-kashe a NajeriyaA daina tsangwama da kuma muzguna wa wadansu 'yan majalisa
*Gwamnati ta rika bin doka da oda
*Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai
*Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah
*Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka shafi majalisar
*Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya don ceto demokradiyyar Nijeriya
*Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya don ceto demokradiyyar kasar
*Shugaban kasa ya magance matsalar rashin aikin yi da kuma talauci a kasar
*Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara
*Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na 'yan sandan Nnjeriya Ibrahim Idris
*Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu.
Wadansu na ganin barazanar daukar matakin da tsarin mulki ya ba su kamar yadda suka yi ikirari zai iya hada wa da yunkurin tsige Shugaba Buhari
A ranar Litinin 'yan sandan kasar suka gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki domin amsa tambayoyi kan zargin daukar nauyin 'yan fashi da makami a mahaifarsa ta jihar Kwara.
Sai dai daga bisani Sanata Saraki ya ce sun shaida masa cewa sun janye gayyatar, kawai suna bukatar "ya amsa ne a rubuce".
Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun fasa ganawa da OsinbajoAPC ta sha kaye a hannun PDP a zaben jihar Oyo
Rahotanni sun kuma ce an rage yawan jami'an tsaron farin kaya da ke bin tawagar Saraki da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da kuma mataimakansu.
Wannan batu ne kuma ya sa kungiyar tsoffin 'yan sabuwar PDP, wacce Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ke kan gaba a ciki, suka ce sun dakatar da tattaunawar da suke yi da gwamnatin kasar da kuma jam'iyyar APC.
Suna dai zargin cewa an mayar da su saniyar-ware ne tare da yi musu bi-ta-da-kulli, a gwamnatin da suka taimaka aka kafa.
A baya dai gwamnatin ta sha musanta wannan zargi.
" Dalilin Da Ya Sa Buhari Bai Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin Bana Ba"
" Dalilin Da Ya Sa Buhari Bai Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin Bana Ba"
___¥___
*
Ministan Kasafin kudi da tsare tsaren kasa, Sanata Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa a halin yanzu Shugaba Muhammad na nazari kan daftarin kasafin kudin 2018 wanda majalisar tarayya ta mika masa.
Ministan ya ce, yin nazarin ya zama dole don zakulo wuraren da aka tafka Kurakurai da aringizo. Tun watan Nuwamba na shekarar 2017 ne, Buhari ya mikawa majalisar kasafin kudin wanda aka tsara kashe Naira Tiriliyqn 8.6.
___¥___
*
Ministan Kasafin kudi da tsare tsaren kasa, Sanata Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa a halin yanzu Shugaba Muhammad na nazari kan daftarin kasafin kudin 2018 wanda majalisar tarayya ta mika masa.
Ministan ya ce, yin nazarin ya zama dole don zakulo wuraren da aka tafka Kurakurai da aringizo. Tun watan Nuwamba na shekarar 2017 ne, Buhari ya mikawa majalisar kasafin kudin wanda aka tsara kashe Naira Tiriliyqn 8.6.
Monday, June 4, 2018
RA'AYI: Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba
RA'AYI: Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba
Daga Zee Taraba
Dan Allah masu yi wa Buhari makauniyar soyayya ida kun isa ku hana Allah ya yi masa hisabi ranar gobe tunda ku ba za ku fada masa gaskiya ba kuma ba za ku bari masu tsoron Allah su fada masa gaskiya ba.
Mun lura abun naku ya soma wuce gona da iri, har ta kai ga kuna zagin Malaman addini akan siyasar banza wadda kwata-kwata duk rantsi duk jimawa shekaru takwas kacal ake akan kujerar.
Mulkin Buhari babu hali Malami ya ce zai fito ya fadawa Buhari gaskiya sai a soma cewa wai malamin siyasa ne, idan kuma ya yaba Buhari sai a ce na addini ne tsabar son zuciya irin namu.
Wai shi Buhari yafi karfi a fada masa gaskiya ne?
A ce wai Malaman addini a ringa zagin su akan wani dan Siyasa wanda kullum shi a yabon kansa yake shi kadai tsabar son rai?
To bara ku ji na fada muku, idan kun hana a fada masa gaskiya a nan gidan duniya, to ku sani baku isa ku hana Allah ya yi masa hissabi ba bisa ga yadda ya gudanar da mulkinsa da kuma rayuwarsa ba ranar gobe.
Saboda haka a yi hattara dan Allah, Siyasa ba hauka bane.
Subscribe to:
Posts (Atom)