spon

Monday, July 9, 2018

JIYA BA YAU BA

JIYA BA YAU BA

AREWA UWAR DADI: Wani ayarin mutane a kan kekuna suna tafiya a Zaria a shekarar 1960.

A lokacin babu ciwon hawan jini.
Allah ya kara mana lafiya.

Madogara: Uwa Idris

Sunday, July 8, 2018

MUSIC: Dj Abba – Bomba Man

The intelligentleman known as Dj Ab came across with another clarified hit dubbed BOMBAMAN.
The YNS frontline artiste is getting the street hot with sequences of songs like NI, DABAN NE & BABBAN YAYA. He is not taking it low as well this time around.


Yanzu An Gama Da Boko Baram, Saura Gyara Yankunan Da Suka Barnata, Inji Buhari


Yanzu An Gama Da Boko Baram, Saura Gyara Yankunan Da Suka Barnata, Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu yankin arewa maso gabas yana matakin daidaita lamurra bayan rikicin Boko Haram.

Da ya ke jawabi ga sojojin Nijeriya a garin Munguno a ziyarar da ya kai jihar Borno a ranar Juma'ar da ta gabata, Buhari ya ce "ta tabbata cewa yanzu muna cikin mataki ne na kokarin daidaita lamurra bayan rikici Boko Haram, kuma hakan ya samu ne saboda kyakkyawan aikin sojojinmu".

Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa mayakan Boko Haram da kansu suke mika wuya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

Bayanin shugaban a Munguno kamar yana nufin an kawo karshen tashin hankalin da jihohin arewa maso gabashin Nijeriya suka yi fama da shi a kusan shekara tara.

Rundunar sojin Nijeriya da gwamnatin Buhari sun dade suna ikirarin kawo karshen rikicin Boko Haram wanda ya yi sanadin salwantar dubban rayuka a arewacin Najeriya tare da raba miliyoyi da gidajensu.

Tun a yakin neman zabensa, Buhari ya alwashin zai kawo karshen rikicin Boko Haram da ya shafi kasashen da suka kewaye tafkin Chadi, Nijar da Kamaru da Chadi.

Sai dai kuma har yanzu Boko Haram na ci gaba da yin barazana a yankunan inda ko a watan da ya gabata an kashe mutane 43 a hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Damboa a jihar Borno.

Kashe-kashen da ake samu a rikicin makiyaya da manoma da kuma harin 'yan fashi a wasu jihohin Nijeriya wani babban kalubale ne na tsaro ga Buhari wanda ya ayyana neman wa'adin shugabanci na biyu.

PDP Ta Kalubalanci Buhari Kan Ya Kori Ministar Kudi Kan Shaidar Yiwa Kasa Hidima Ta Bogi

PDP Ta Kalubalanci Buhari Kan Ya Kori Ministar Kudi Kan Shaidar Yiwa Kasa Hidima Ta Bogi
__¥___
*
Jam'iyyar PDP ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan ya gaggauta korar Ministar Kudi, Kemi Adeosun tare kuma d hukunta ta bisa amfani da shaidar kammala bautar kasa (NYSC) ta bogi.

Sakataren Jam'iyyar na Kasa, Kola Ologbondiyan ya ce a halin yanzu ta tabbata cewa gwamnatin Buhari na cike da barayi, 'yan damfara da mutane marasa gaskiya inda ya jaddada cewa kada Buhari ya kuskura ya kyale Ministar wanda yin hakan zai nuna cewa ba da gaske yake yi ba game da shirin yaki da rashawa da ya kaddamar.

Saturday, July 7, 2018

[Video] Dadin Kowa Sabon Salo Episode 61 Arewa24


Domin cigaban shirin dadin kowana wannan satin kawai kukasancedamu.
A CIKIN WANNAN SATIN:
Rana tsaka Malam Nata’ala ya hadu da gamonsa bayan da wani tsohon dan dambe ya ziyarce shi.
Danliti Shagon gabas ya zo ne domin ya tafi da dansa Datalle, sai dai an nemi Dantalle sama da kasa an rasa, wanda hakan ya jefa Malam Nata’ala cikin Cakwakiya.

[Music] Ado Gwanja -Masoyana

Sabuwar wakar Ado Isah Gwanja Mai Suna ” Masoyana ” waka mmai dauke da nishadantarwa masamman mata kusan nakune wannan kawai ku saurareta kuji.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Hayye masoya bani da tamkarku
– Kufito inai muku fatan alkairee
– Hayye maza da mata ni banda irinku

– Gwana inai muku fatan alkairee
– Hyy ku fito kuzo kuji babban labari
– Ku tsaya kuga sabon tsari
– Ado na gwanja na yaba alkairi
– Domin nayi kazo dashi a cikin layi

Sunday, July 1, 2018

Video: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 60 Arewa24



Domin kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya wuce
A Satin Da Yaga Bata:=
DANBABA ya shiga hannu, ko wane mataki ALH BUBA zai dauka? Asirin ADAMA ya tonu a gaban KAMAYE kuma KAMAYE ya dau zafin da bai taba dauka ba.
KYAUTA ta hadiyi kaya daga wurin su GAYE wadda ta makale mata.
Su IB sun sa himmar yaki da abinda ya addabi al’umarsu.
BINTU tayi nisa bata jin kira, inda IB yake kokarin ceto ‘yar’uwarsa.
A Cikin Wannan Satin Sai Dai kun kalla.





DOWNLOAD VIDEO