Har yanzu tauraron fitacciyar jaruma Rahama Sadau na cigaba da haskawa inda ya samu wani sabon lambar yabo a karshen makon da ya shude.
Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar 22 ga watan Satumba a dakin taro na Transcorp hilton Hotel dake Abuja.
Rahama ta nuna farin cikin ta samun wannnan kyautar a shafin ta na kafafen sada zumunta.
Gasar Peace Achievers Awards biki ne wanda aka gudanar a ko wani shekara domin karrama fitattun hukumomi da yan kasar dake taka rawar gani wajen raya zaman lafiya a kasar.
Bikin gasar na bana shine karo na bakwai.
Kyautar da jarumar ta samu shine na uku da zata samu bana bayan na jaridar Leadership da gidauniyar Global Women Empowerment network