Thursday, December 28, 2017
Trump ya amince da sayar wa Nigeria jiragen yaki
Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen yakin guda 12 samfurin A29 Super Tucano a cikin wata wasika sa ta aikewa rundunar sojan samar kasar.
Da yake gabatar da wasikar, jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington ya bayyana kudurin gwamnatin kasarsa na taimakawa Najeriyar cin galaba kan mayakan kungiyar Boko Haram.
Ya kuma ce wannan ya hada da taimakawa Najeriya kawar da duk wani nau'in ta'addanci daga cikin iyakokinta.
Jakadan na Amurka ya ce ko baya ga sayar da jiragen, gwamnatin kasarsa a shirye ta ke ta taimakawa rundunar sojin saman ta Najeriya a kokarin da take yi na kara karfafa mayakanta ciki har da rika samar mata da kayayyakin gyara da kuma tattalin jiragen.
Gwamnatin ta Donald Trump kuma ta ce a shirye take ta mika wa Najeriya wadannan jiragen tun da wuri amma sai ta biya kudinsu lakadan.
Babban hafsan sojan saman Najeriya Air Marshall Sadique Baba Abubakar, wanda ya karbi wannan wasikar a madadin rundunar ya yaba da wannan mataki na Amurka.
Ya kuma ce ba da bata lokaci ba zai bayar da sunayen matuka da kanikawan jiragen yakin rundunar domin a ba su horo a kasar ta Amurka kan yadda za su sarrafa wadannan jiragen.
A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labarai na rundunar sojan saman ta Najeriya Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya ta ce ana sa ran kammala sa hannu a kan yarjeniyoyin cinikin da kuma biyan kudin jiragen kafin ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2018.
Gwamnatin Donald Trump ta amince da bukatar sayar wa Najeriya wadannan jiragen yakin domin yakar kungiyar Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Tun a shekara ta 2014 ne Najeriya ta bukaci sayen jiragen daga kasar ta Amurka.
Amma a wancan lokacin gwamnatin tsohon shugaba Barrack Obama ta ki amincewa da hakan saboda damuwar da take da ita cewa mai yiwuwa a yi amfani da makaman wajen keta hakkin bil adama.

George Weah ya lashe zaben Liberia
Tsohon shahararren dan kwallon kafa George Weah ya lashe zaben shugaban kasar Liberia.
Bayan da aka kidaya kuri'u daga kusan dukkan mazabun kasar, kuma bayan zaben da aka yi a zagaye na biyu, George Weah ya tserewa abokin karawarsa, Joseph Boakai nesa ba kusa ba.Zai gaji Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da aka taba zaba a matsayin shugabar kasa a Afirka, kuma a zaben demokradiyya na farko da zababbe zai mika wa wani zababben tun bayan yakin basasar kasar.
Mrs Sirleaf ta doke Mista Weah a zaben shugaba kasar da aka gudanar, shi ma a zagaye na biyu, a 2005 bayan yakin basasar kasar.
Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.
Yakin neman zaben Mista Weah a karkashin hadakar jam'iyyun siyasa ta CDC - Coalition for Democratic Change - ya burge matasa sosai, amma abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Mista Boakai bai sami karbuwa sosai ba.
Kuma matar tsohon shugaba Charles Taylor, Jewel Taylor ce mataimakiyarsa, duk da cewa shi Charles Taylor din na tsare a wani gidan yari dake Burtaniya a sanadiyyar samunsa da laifukan yaki da aka yi a makwabciyar kasar Saliyo.
A watan Oktoba, Mista Weah ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda ya sami kashi 38.4 cikin dari, shi kuwa mai binsa a baya, Mista Boakai dan shekara 73 ya samu kashi 28.8 cikin dari.
Rashin samun wanda yayi nasara kai tsaye ne ya janyo aka gudanar da zaben a zagaye na biyu.
Hukumar zaben kasar ta Laberiya ta ce an kammala kidayar kashi 98.1 cikin dari na kuri'un da aka kada, kuma zuwa ranar yau Alhamis, Mista Weah ya lashe kashi 65.5 cikin dari na kuri'un.
Mista Boakai kuma na da kashi 38.5 cikin dari ne na dukkan kuri'un.
Mista Weah ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa kamar AC Milan da Chelsea da Paris St-Germain, kuma shi ne dan Afirka tilo da ya taba lashe lambar dan wasa mafi shahara a duniya da kungiyar FiFA ke bayarwa da kuma lambar Ballon D'Or.
Ya shiga siyasa bayan da ya daina buga wasan kwallo a 2002, kuma a halin yanzu yana rike da mukamin sanata ne a majalisar Laberiyan.
Kararraki da aka shigar a kotu ne suka hana a gudanar da zaben a watannin baya, kuma masu kada kuri'a basu fito sosai ba.
Jami'an zabe sun ce kashi 56 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a ne suka fita zuwa rumfunan zabe.
Fiye da mutum miliyan biyu ne suka yi rajista a kasar ta Laberiya mai mutane kimanin miliyan 4.6.
Mrs Sirleaf ta zama shugabar kasa a 2006 bayan da 'yan tawaye suka fatattaki Charles Taylor a 2003, dalilin da ya kawo karshen yakin basasar kasar.
A halin yanzu Charles Taylor na zaman kaso na tsawon shekara 50 a Burtaniya saboda laifukan yaki dangane da yakin kasar Saliyo.

Karanta yadda ake 'cin zarafin matan Nigeria a Facebook'
Wani bincike ya nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma'abota shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook.
Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na tauye 'yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da shi. Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al'umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.
Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Muhammad Awwal Garba daga hukumar Hisbah ta jihar Kano da Maryam Ado Haruna, jami'a a wannan cibiya ta fasahar sadarwa da aka fi sani da CITAD, inda suka yi masa bayanin yadda girman matsalar take.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar tasu:

Wednesday, December 27, 2017
Dan Shugaba Buhari ya karye a hatsarin babur
Yusuf Buhari, dan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mummunan hatsarin babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin ranar Talata da daddare.
A cewar Garba Shehu, "Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki".
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari da mai dakinsa Aisha suna godiya ga 'yan Najeriya bisa addu'ar da suke yi wa dan nasu.
'Ya'yan masu hannu da shuni kan yi wasan tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da hatsari.
A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta haramta yin irin wannan tsere bayan wasu rahotanni da aka samu na tukin ganganci da masu tseren ke yi.
Subscribe to:
Posts (Atom)