spon

Showing posts with label FOOD MAKING. Show all posts
Showing posts with label FOOD MAKING. Show all posts

Wednesday, October 10, 2018

Kalli:yadda ake kala kalar shayi

 

????TABA KA LASHE????

TEA☕☕☕☕

☕PINEAPPLE TEA
????Abarba
????bawon Abarba 
????citta 
????kaninfari
????ganyen shayi

Ki bare abarbarki ki yanki kadan bada yawa ba ki hada Da bawon abarbar ki zuba a tukunya, bayon yafi abarbar yawa saiki saka citta Da kaninfarin da kika dan daddakasu ki saka Lipton ki hada ki tafasa sosai kisa sugar sai sha ????


GORIBA TEA☕☕☕☕

????Goriba 
????citta 
????kaninfari
????bawon bayan lemon zaki 
????Lipton 

Zaki samu goriba irin ba rarriyar nan wadda aka fiddata daga jikin kwallonta saiki wanketa kisa a tukunya ki zuba citta Da kaninfari sannan ki samu bawon lemo ki dan gogashi a ciki Da abun goga carrot, ammafa karki cika dayawa dan kamshin muke bukata kadan saiki saka Lipton Da dan sugar ki barsu suyi ta dahuwa, saikin barshi ya dahu sosai komai najikin goribar ya futo sosai, wannan shayin nada dadi sosai kuma yana karama maza Da mata lafiya kwarai Da gaske.

SHAYIN DANYAR CITTA DA LEMON TSAMI☕☕☕☕

????Danyar citta 
????Lemon tsami 
????Lemon grass 
????kaninfari 
????Na, ana, a
????Lipton 

Ki goga cittarki dai dai misali ya danganta Da yadda kikeson yajinta ki saka Lemon grass Da na, ana, ki yanka Lemon tsaminki gida biyu ko jefa a ciki kisa Lipton da sugar ki tafasa sosai. In kina Da bukatar tsamin kya iya matsa ruwan lemon tsamin in kinxo sha. 

CINNAMON AND HONEY TEA ☕☕☕☕☕
????cinnamon (girfa) 
????honey (zuma) 
????citta 
????kaninfari 
????lemon grass 

Ki zuba ruwa a tukunya ki zuba garin cinnamon ko wanda ba nika ba ki saka kaninfari Da citta Da Lemon grass ki tafasa sosai, inya dahu ki zuba zuma ki barshi yayi tafasa daya saiki sauke

Wednesday, September 5, 2018

KOKUNSAN YACCE AKE DANKALI + NAMA

KOKUNSAN YACCE AKE DANKALI + NAMA

AUTHOR /AREWAIFINIT
 DATE/5 SEP 2018
KAYAN HADI
  • Dankali
  • Nama
  • Kwai
  • Attaruhu
  • Albasa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyaďa
  • Fulawa ko garin busashen buredi
*YADDA AKE HADA WA*
Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast dashi.
KOSAN DANKALI
*KAYAN BUKATA*
  • Dankalin turawa 
  • Nama
  • Fulawa
  • Kwai 
  • Albasa 
  • Attarugu
  • Gishiri 
  • Maggi
  • Man gyada

*YADDA AKE YI*
Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi matuka...

Tuesday, September 4, 2018

YACCA AKE HADA ILOKA

AUTHOR/AREWAINFINIT
DATE 4SP2018

INGREDIENTS:
  • 1. Madara gwangwani biyu
  • 2. Sugar gwangwani ďaya da rabi
  • 3. Oil
PROCEDURE: A zuba mai kamar cokali biyu a tukunya sai a zuba ruwa kamar rabin kofin roba, sai a juye madara da sugar, a jujjuya har sai an ji sugar ya narke sannan a ďaura a wuta. Zai yi ta dahuwa yana tasowa ke kuma kina juyawa don kada ya zuba idan ruwan ya fara yin qasa madarar ta fara soyuwa sai ki zuba mai kamar table spoon biyu ki cigaba da juyawa, in ya fara yin brown sai a rage wuta, a cigaba da juyawa. In kina so yayi qarfi sai kiyi ta soyawa har sai yayi golden brown sosai. In kuma mai taushi ki ke so kamar nawa idan colour sa ya koma brown duka kuma kina juyawa kina jin ya qame babu alamun ruwa sam a jikinsa sai a sauke.
A shafawa leda mai sai a juye a kai, a bar tukunyar akan wuta sai a rinka saka cokali a na kwashe sauran. Daga nan sai a mulmula irin yanda ake so a yayyanka. Amma in me karfi ne ba zai yiwu a bari ya huce ba. Da zafi zafin sa za a rinka mulmulawa in ba haka in ya sha iska ba zaki iya gutsiran sa ba. Ina son iloka fiye da tuwon madara don yana ďauke mun kewar goody-goody.

Sunday, September 2, 2018

YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
 TITTLE YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI.
KAYAN HADI*
  • Kwai
  • Kifi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Fulawa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyada
 
*YADDA ZA KIYI*
Da farko ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki ďora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cicire 'kayar shi sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, ki fasa 'kwai kaďan ki zuba a ciki, ki ďauko fulawa ki zuba(hikimar sa fulawa dan ya haďe jiki ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe
 
SPINACH EGG SAUCE

INGREDIENTS:
1. Spinach (Alayyaho)
2. Eggs, oil
3. Tattasai, tarugu, albasa and garlic.
 
PROCEDURE: A wanke alayyaho a yayyanka qanana, sai a yayyanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko zaki samu tukunyar da babu komai a wuta ki juye alayyahon duka ki ďan turara sa. In kina da steamer zaki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.
Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in ya ďan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu ki juye alayyahon ki jujjuya su hade.
Ki kaďa eggs ki juye a ciki ki juya su haďe da kyau, in ya gama soyuwa sai ki sauke. Zaki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma doya da dankali.
Note: Zaki iya zuba isashen kwai ni nafi son shi a haka. Ba dole sai spinach ba zaki iya yi da sauran ganyayyaki. Kuma zaki iya yi babu kayan miya, idan kika yi steaming alayyahon tare da albasa sai ki kaďa kwai ki juye a ciki. A kula sosai idan kin yanka alayyaho ne kafin ki yanka to ki zuba ruwa isashe yanda zai taso sama sai ki kwashe zaki ga qasan ya koma qasa in ba haka ba zaki rinqa ci kina jin qasa. Yana da dadi in aka sanya a shinkafa. Ga kuma qara lfy.
 
Gashashen Kifi/ Grilled Fish
Kayan Hadi:
1. Kiyin Karfasa / Tilapia
2. Albasa, lemun Tsami, Citta, Kanunfari, Masoro, Tafarnuwa, Garin Yaji ko Tarugu.
3. Maggin Knorr, Gishiri, Kori, Thyme, da kayan Qamshi da Dandano
4. Myan Gyada.
Yadda Zaki Sarrafa: Ki wanke kifin ki ciki da bai, saka hannu har cikin bakin kifin ki wanke shi sosai. Bayan kin wanke sai ki tsane ruwan in sauri kike yi kisa towel ko tissue ki cire ruwan.
Daga nan sai ki daka ko kiyi blending kanunfari da masoro, citta, thyme, da sauran su. In kuma kina da garin su shikenan. Sai ki juye a mixing bowl.
Sannan ki dauko albasa kamar rabi haka ki saka, ki zuba tafarnuwa biyu manya, idan ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi blending ko daka yayi luqui luqui. Haka nan in tarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi.
Daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba curry kadan, ki zuba knorr da gishiri, sannan ki matse lemun tsami qaramin cokali daya ki zuba. Sai ki zuba oil yanda hadin zai kama jikin kifin.
Bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki. Sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a fridge yayi kamar minti 30 in a freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi qanqara ba.
Daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da oven ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin ki, kina yi kina jujjuya wa har ya gazu.
Hadin Sauce/Sauce
Kayan Hadi:
1. Albasa biyu ko uku
2. Tarugu, Tattasai da Green pepper
3. Tafarnuwa 1
4. Gishiri da Maggi knorr
Yadda Zaki Hada Sauce: Farko zaki yanka albasanki da tattasai da green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura mai a tukunya kamar quater qaramin ludayi, in yayi zafi ki zuba albasan da tattasan, ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba niqaqqen tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa tare da sinadarai, sai ki dan zuba ruwa kadan yanda zasu dahu. Zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida.
Daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din a sama. Ai haka zaki ji kawai yana shigewa cikin tumbin maigida yana santi.
Kada a manta a ajiye wa mai gida lemun tsami na wanke hannu bayan ya gama ci saboda qarni. Sannan a tabbata an saka ginger ko citta, tafarnuwa da kanunfari don suna da muhimmanci a gashi.

YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
      TITTLE:YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

Abubuwan hadawa

  • Semonvita kofi 1/2
  • Madara cokali 6
  • Suga dai dai dan dano

Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tukunyarki, ki sa ruwa ki dora a wuta ya tafasa.
  2. Sai ki dauko semonki ki dama da ruwa ya yi kamar za kiyi talge.
  3. Sai ki duba idan ya tafasa sai ki zuba a kan ruwan ki juyashi sosai.
  4. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba a kwano ki sa madara da suga sai ki juya ki zubawa kowa a kofi.

A sha dadi lafiya. Na gode sai mun hadu girki n a gaba.