spon

Monday, April 2, 2018

Kannywood: Ni Da Sake Yin Aure Ba Yanzu Ba – Inji Fati Kk

Tun ba yau ba ake rade-radi kan mutuwar auren ta wanda ya sanya har ta kwaso kayanta daga Kano zuwa Kaduna, garin iyayenta.Auren ta na biyu da tsohon mijinta wanda yayi sanadiyar komawar ta Kano, Allah ya albarkace su da yara biyu,Ahmed da Yasmin.

A hirar ta da wakilin jaridar Leadership Ayau, Fati KK ta fayyace masa labarin dalla-dalla kan yadda al’amura suka kasance har suka rabu da mijinta.

“To ni dai abin da zan iya cewa, ni dai har ga Allah ya sani, wadanda muke tare da su su ma sun sani, na so zaman aure.In da ba na son zama da shi, wallahi ba zan mike kafafu na yi ta zuba ‘ya’ya ba. Na fuskanci gori daban-daban duk na shanye, kuma hakan bai sa ni bijirewa ba har na ce a sake ni ba, na kan zauna in yi kuka, watarana sai na fada masa, sai na gane in har wani ya ki ka, ai Allah na son ka. Na fuskanci kalubale kala-kala, sai dai in ce mun gode Allah.”

Jarumar wacce aka daina jin duriyarta a fagen shirya fim bayan auren ta ta bayyana cewa dangin mijinta sun zargi ta da bijire ma mijinta bayan ta samu labarin cewa zai kara aure. Tace basu fahimce ta ba domin bata da kishin samun kishiya. Haka zalika bazata zabi rabuwa da mijinta kan matsalar rashin kudi/talauci.

“Mun haihu da shi yara biyu, Abu ya ki ci, ya ki cinyewa, a gaskiya talauci bai taba sa na ce zan rabu da wanda nake tare da shi ba. Na dai samu surutai a cikin danginsa, wai don zai kara aure ne na bijire masa na ce ya sake ni, alhalin wallahi tallahi, wallahi tallahi, wallahi tallahi ban san wannan zancen ba, ban ma taba jin sa ba. ”

Kannywood: Babu Mace Mai Dadin Zaman Aure Kamar ‘Yar Fim – Ladidi


A duk lokacin da aka dauko batun aure, wasu da yawa kan yi wa ‘yan fim gani-gani. To amma a wannan karon magana ta kare, domin jarumar da muka tattauna da ita a wannan makon ta ce rashin sani ne ke sa mutane kyamatar auren ‘yan fimIdan mutum ya fahimci lamarin kuwa, zai fi wadanda ke auren wadanda ba ‘yan fim ba jin dadin zaman aure, ko me ya sa?

Sammam Masu karatu ko kun san shahararriyar jaurmar wasan kwaikwayon ta taba yunkurin shiga aikin soja kafin ta fara wasa?

A karanta firar duka a Taurarin Nishadi
Muna so mu ji cikakken tarihin rayuwarki
Ni dai sunana Ladidi Abdullahi An fi sani na da suna Tubeeless. An haife ni a Kaduna a wata unguwa da ake kira Sabon Gari Nassarawa, wato dirkania ke nan. Na yi Furamare wato a Nassarawa na kuma je makaratar gaba da Furamare.duk a Kaduna wato, ina gama sakandare aka yi min auren fari sai Allah bai yi zamana da mijin ba, sai muka rabu.




Daga nan sai na ji ina son yin aikin kaki, na je na sayi ‘form’ din aikin soja na ruwa na cika na ba da aka kira mu, na je duk abubuwan da ake yi na yi daga, baya ban sake bin ta kan shi kuma ba saboda oda wasu dalillai.

Yaushe kika fara fim din Hausa, da wane fim kika fara, kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga?

Wata rana sai Rabi’u Rikadawa ya zo gida ya same ni ya ce min, ki zo mu je ki yi aikin fim, shi da Obina. Na ce musu ku je zan zo,
Amma sai na ki zuwa na neme su. Sai muka hadu da Zainab Abubakar muna hira ta ce min, ki zo mu yi aikin fim mana. Na ce mata zan bi ki. Ta ce, min, duk ran da za ta yi aikin za ta kira ni mu je mu yi tare. Na ce mata ba damuwa. kuma kafin nan, muna Hausa ‘drama’ a makaranta dama. Ran da Alfa ‘care’ zai yi wani fim sai ta ce na zo mu je.

Na ce mata to, muka je muka gana, sai shi ya tambaya da ma ina fim ne?

Saboda ya ga ba na kuskure. Daga nan sai na muka cigaba da zuwa N TA. Oganmu George ya ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani. Daga nan kuma ’yan Kano suka zo Kaduna za su yi wani flm sai aka kira ni. Kafin nan mun yi wani flm wanda Rabi’u Koli ya sa Wada Rikadawa ya kira na yi, sai na ciga da aiki sai aka cigaba da kira na ina yi, shi ne. Sai dai na manta shekarar gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi wani fim Balarabe da Balarabe dila ya kira ina Abuja ya ce na je Kaduna za mu yi wani fim. Shi ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni, na ce musu ina zuwa nako zo muka yiFim din da na fara na Turanci ne, shi ne na Alfa ‘care’.


Thursday, March 29, 2018

Music: Husaini Danko – Na Dasa Buri

Sabuwar wakar husaini danko mai suna ” Na dasa buri ” wakar gaskiya tayi dadi sosai ba’a magana kawai asha waka banda magana kai idan ta kama ayi rawa ayi kawai.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Na dasa buri da alaka inda rabon zan samu
– Karnaji kunya naki nuni inrasa kokon madara
– Ahh ba’a rabamu tunda na nunaki
– So ya hadamu naki nauyin baki
– Kekika ce dani ina burgeki


Kin zama kwal da babu mai canza ki
– Zuciyace tace ina gadinki
– Rai ya ajeki bangaran sa dauki
– Shi kuma baki so ne mai hora
– Ahh Kwana a tashi an saba
– Wanda ya tara ke diba
Domin jin sauran baitikan ai kawai ku sankamota dan saurara.

Wednesday, March 28, 2018

Music: Salisu SA Maiwaka – Likimo


Tuesday, March 27, 2018

Music: Abdul D One Ft Umar M Shareef – Abun Mamaki MUSIC






Film Din ‘Yar Mai Ganye Ya Fito Kasuwa

Fim Din ‘Yar Mai Ganye Ya Fito Kasuwa
Daya daga cikin Fina-Finan Kannywood da ya samu ingantaccen aiki wanda aka jima a na jiran fitowarsa wato ‘Yar Mai Ganye ya fito kasuwa a ranar yau Lahadi.
‘Yar Mai Ganye fim ne da mata suka baje kolinsu tare da cin duniyar su da tsinke tamkar an halacce su domin su bautar da maza.
Sabon Fim din ‘Yar Mai Ganye shine ne irinsa na farko da mata ke sarrafa mazajen su son ransu. “Gashin aya a tafin hannu abubuwa ne da magidanci ya fuskanta a fim din.”
Shin ku na son ganin yadda uwar gida ke juyawa tare da sarrafa mijinta son ranta yadda take so? Kuna son ganin yadda maigida ke dafa abinci, ya share gida ya wanke motar uwar gida, idan kuma ya ki aradu ta far masa? To ku nemi ‘Yar Mai Ganye.

“Ko ba komai mata iyayen giji, in ba ku ba gida, idan kuma kun yi yawa gida ya gyaru. Duk da irin baiwar da Allah ya yi masu ta sarrafa mazaje a tafin hannun su amma sun zabi bin bahaguwar hanya domin cimma biyan bukata ta barauniyar hanya.”
‘Yar Mai Ganye fim ne kan yadda Hadiza Muhammad (‘Yar Mai Ganye) ke amfani da karfin bokanci wajen taimakawa mata domin su mallake mazajen su cikin ruwan sanyi tare da mayar da maigida kwatankwacin mijin ta-ce ko mijin kafin- ta – ce.
Ali Gumzak SAK fitaccen Daraktan da tauraruwarsa ke haskawa daidai da farin wata ne ya bayar da umurnin fim din a yayin da fitacce kuma kwararren hazikin Furudosa mai tashe wato Abdul’aziz Dan- Small ya shirya fim din ‘Yar Mai Ganye. Tsinin Alkalamin Masanin Sirrinsu kuma shahararrren marubuci nan na jiya wanda ake jin amonsa a duniyar yau Maje El-Hajeej Hotoro ne ya rubuta tare da tsara labarin. Shi kuwa Dan Kasuwar Kasa da Kasa Alhaji Yusuf Yunusa ya dauki nauyin shirya fim din a karkashin kamfaninsa BGM FILM PRODUCTIONS.
Jaruman da suka jagoranci shirin ‘Yar Mai Ganye sune da Hadiza Muhammad, Rabi’u Rikadawa, Aina’u Ade, Halima Atete, Sulaiman Bosho, Hajara Usman, Saratu Gidado, Nuhu Abdullahi, Jamila Nagudu, Sadiya Adam, Maryam Yahaya, Amar Umar tare da gabatar da sababbin fuskoki biyu wato Momi Chiroma da Lubabatu Muhammad.
‘Yar Mai Ganye Fim ne da aka yi wa ingantaccen aiki a kololuwar mataki na kwararru wanda kuma aka sanya natsuwa tare da zabar ‘yan wasa a bisa ga kwarewa da cancanta. Tabbas hakika ‘Yar Mai Ganye fim ne da da zai kayatar ya kuma burge mai kallo.

Music: Husaini Danko – Basani Ba Sabo


Sabuwar wakar husaini danko kenan mai suna ” Basani Ba Sabo ” wanda wasu suka jima suna jiranta to yau gata mun kawo muku ita.
Gaskiya oga husaini kasan darajar bawa masoya nishadi a wajan kida dan baka saurarawa Ganga.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Yau basani ba sabo
– Munada sabon zance
– A zuciya hujjarmu
– Da namu bama rance
– Wanda kayiwa a yau ke zaginka




– Idan Gabanka yazo bai kusheka
– Idan yana da bukatar hajarka
– In yabarka ya hau tan bihinka
– Sai ya dinga fadin ya haskaka
– Wai shi yasa wasu ke saurararka
– Har ya manta gwanine taskarka
– Idan yabaka ina mai tureka
Kai danko Allah ya saka da alkairee a cigaba da basu sakonni na fadakarwa