spon

Sunday, June 3, 2018

Mun kusa hadewa da wasu jam'iyyun adawa don fatattakar APC a 2019 - PDP

Mun kusa hadewa da wasu jam'iyyun adawa don fatattakar APC a 2019 - PDP

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Prince Uche Secondus ya shaidawa wakilin kamfanin jaridar Punch cewa tuni shirye-shiryen hadewa da sauran jam'iyyun adawa a kasar nan domin kawar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019 yayi nisa.

Shugaba Secondus ya bayyana cewa kwamitin da jam'iyyar ta kafa karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas na samun gagarumar nasara don kuwa tuni sun kai wani mataki na fahimtar juna da wasu jam'iyyun.

Mun kusa hadewa da wasu jam'iyyun adawa don fatattakar APC a 2019 - PDPKU KARANTA:An mallakawa Yarima Bin Salman ikon Makka da Madina

Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su

Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su

A yau ne hukumar ‘yan sanda ta aike da takardar gayyata ga shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, bayan wasu gungun ‘yan fashi da aka kama sun bayyana cewar Saraki na daga cikin mutanen da suke yiwa ayyukan ta’addanci.

Hukumar ta ‘yan sanda tace yanzu haka tana tsare da mutane 22 da take zargi da hannu cikin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu tare da kashe mutane kimanin mutumin 33.

Ga jerin sunayen mutanen da inda suka fito kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta wallafa

Sugabannin gungun 'yan fashin shine:
1. Ayoade Akinnibosun,mai shekaru 37 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.

2. Ibukunle Ogunleye, shekaru 36 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

3. Adeola Abraham, shekaru 35 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 5

4. Salawudeen Azeez, shekaru 49 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

5. Niyi Ogundiran, shekaru 37 –daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.
Ya kashe mutane 2

6. Michael Adikwu,shekaru 30 – Ya kashe mutane 22, yawancin su 'yan sanda.

7. Kabiru Afolabi, shekaru 26

8. Omoseni Kassim, shekaru 28

9. Kayode Opadokun, shekaru 35

10. Kazeem Abdulrasheed, shekaru 36

11. Azeez Abdullahi, shekaru’ 27

12. Adewale Popoola, shekaru 22

13. Adetoyese Muftau, shekaru 23

14. Alexander Reuben, shekaru 39

15. Richard Buba Terry, shekaru 23

16. Peter Jasper Kuunfa, shekaru 23

17. Ikechukwu Ebuka Nnaji shekaru 29

18. Moses Godwin, shekaru 28

19. Adeola omiyale, shekaru 38, daga garin Isanlu Isin, Isin LGA, Kwara State.

20. Femi Idowu, shekaru 34

21. Alabi Olalekan, shekaru 49-mai taimakawa gwamnan jihar Kwara na musamman

22. Yusuf Abdulwahab, shekaru 58 –Shugaban ma'aikatan jihar Kwara.

Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda ya kama Saraki

Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda ya kama Saraki

A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi masa da zarar takardar gayyatar ta same shi.

Kazalika, Saraki ya musanta cewar akwai wata alaka dake tsakanin sa da mutanen da ake zargi da aikata laifin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.

A yau, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu daga cikin wadanda ta kama dangane da batun fashin bankunan garin Offa sun ambaci sunan Saraki da na gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a matsayin mutanen dake daukar nauyin aiyukan su na ta’addanci.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya , Ibrahim K. Idris, ya kama Saraki bayan gabatar masa da shaidar samun hannun Saraki a cikin aiyukan ta’addanci, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Zuwa yanzu Kakakin shugaban kasa da na hukumar ‘yan sanda sun ki cewa komai a kan wannan batu dama kuma batun ganawar shugaba Buhari da shugaban na ‘yan sanda ta ranar juma’a.

Da yake jawabi cikin sanarwar da mai Magana da yawun sa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar, Saraki yace alakanta shi da fashi wani makirci ne kawai na bata masa suna.

An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

A jiya Juma'a ne dai wasu 'yan bindiga suka kashe Mutane har 23 a jihar Zamfara a kauyen Zanoka bayan da suka budewa mazauna kauyen wuta kan mai Uwa da wabi sannan kuma suka cinnawa Gidajen Mutane wuta suka kone kurmus.

Barayin dai sun zo ne kan Babura a matsayin daukar fansar korar da 'yan sintirin yankin su kayi musu inji shugaban karamar hukumar yankin da abin ya faru Mustapha

"Yanzu haka mun binne mutane 23 ciki har da 'yan sintiri da su kayi kokarin dakatar da su."

Mustapha Muhammad ya bayyana cewa 'yan Bindigar sun fara kai farmakin ne ranar Juma'a inda har suka kwacewa Mutane shanunsu sai dai jami'an sintiri na yankin sun fatattake su sannan suka kwato shanun, a dole suka tafi.

Amma sai dai 'yan awanni kadan bayan faruwar hakan sai Barayin suka sake dawowa da babbar runduna kauyen dake nisan Kilomita 160 daga babban birnin Gusau

Kakakin rundunar 'Yan sanda na jihar ta Zamfara Muhammad Shehu ya shaida cewa sun samu gawawwaki 15 bayan da 'yan Bindigar suka kai harin.

"Mafi yawan wadanda suka Mutun 'yan sintiri ne na yankin da su kayi kokarin dakatar da su."

Barayin sun sha kai hare-hare domin sace shanun Mutane tsawon shekaru da dama su kuma kashe duk wani wanda ya nuna tirjiya ga abinda suka aikata.

Wadannan har-hare da ake kai musu ya sanya 'yan Kauyen suka kafa kungiyoyin 'yan sintiri domin tabbatar da tsaro a yankin, amma sai dai su kansu 'yan sintirin ana zarginsu da cin zarafi da kashe wadanda suka kama bisa zargin su.

Yawaitar aiyukan tsagerun ma ya sanya Gwamnati ta kai rundunonin tsaro jihar domin tabbatar da dawo da doka da oda, amma sai dai har yanzu lamarin na dada kamari.

Yaran comedy: Ramadan Kareem Episode 1

Yaran comedy: Ramadan Kareem Episode 1

WA insune suna zaune suna zancen azumi ana zaune sai ga wani mutumi yatawo yana tangadi yana zuwa daidai dasu saiya wadi sai suka tashi sukayo kansa wani yaje yadauko sanda wani yadauko ruwa a buta sai mai sanda yadaga zai bugamasa sai aka rikemasa hannu sukace Kai badan giyabane azumine sai aka yayya famai ruwa ana yayyafa Mai sai yafara nuna bakinsa azuba mai ruwa kasan mai yafaru go an watching TV 📺

Hotunan yadda Aisha Buhari ta yi buda baki da shugabannin Mata

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa.
Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa a ranar Asabar
Buda bakin ya samu halartar mata daga kungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida da kungiyoyin addinai da sauransu.
Daga cikin wadanda aka gayyata buda bakin har da BBC, kuma Raliya Zubairu da Fatima Othman ne suka wakilci BBC
A wajen buda bakin, Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari da uwar gidan mataimakin shugaban kasa sun gabatar da jawabi

Tsakanin Gwamna Taraba Da Maman Taraba : Ina masu fada saboda yan siyasa? Yanzu mun hankalta?

Tsakanin Gwamna Taraba Da Maman Taraba : Ina masu fada saboda yan siyasa? Yanzu mun hankalta?

Lokacin da maman Taraba Hajiya Jummai Alhassan ke neman kujerar gwamnan Taraba da ita da Gwamna mai ci Darius Ishaku abin ya tashi daga APC da PDP inda abin ya koma na addini.

Daga baya daya kayar da ta sai Buhari ya bata Minista.
Shi yana gwamna ita Minista duka suna samun kudade.

Bayan shekaru kadan sai tace Atiku ne mai gidan ta kuma ko ina zata iya bin shi ta kyale Buhari.

Yau gashi gwamnan Taraba da Maman Taraba suna rike da hannun juna.

Ina magoya bayan nasu daga yan APC da PDP, musulman da kiristocin?
Na tabbata da yawan su na nan babu aikin yi.