spon

Tuesday, June 5, 2018

" Dalilin Da Ya Sa Buhari Bai Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin Bana Ba"

" Dalilin Da Ya Sa Buhari Bai Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin Bana Ba"
___¥___
*
Ministan Kasafin kudi da tsare tsaren kasa, Sanata Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa a halin yanzu Shugaba Muhammad na nazari kan daftarin kasafin kudin 2018 wanda majalisar tarayya ta mika masa.

Ministan ya ce, yin nazarin ya zama dole don zakulo wuraren da aka tafka Kurakurai da aringizo. Tun watan Nuwamba na shekarar 2017 ne, Buhari ya mikawa majalisar kasafin kudin wanda aka tsara kashe Naira Tiriliyqn 8.6.

Monday, June 4, 2018

RA'AYI: Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba


RA'AYI:  Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba

Daga Zee Taraba

Dan Allah masu yi wa Buhari makauniyar soyayya ida kun isa ku hana Allah ya yi masa hisabi ranar gobe tunda ku ba za ku fada masa gaskiya ba kuma ba za ku bari masu tsoron Allah su fada masa gaskiya ba.

Mun lura abun naku ya soma wuce gona da iri, har ta kai ga kuna zagin Malaman addini akan siyasar banza wadda kwata-kwata duk rantsi duk jimawa shekaru takwas kacal ake akan kujerar.

Mulkin Buhari babu hali Malami ya ce zai fito ya fadawa Buhari gaskiya sai a soma cewa wai malamin siyasa ne, idan kuma ya yaba Buhari sai a ce na addini ne tsabar son zuciya irin namu.

Wai shi Buhari yafi karfi a fada masa gaskiya ne?

A ce wai Malaman addini a ringa zagin su akan wani dan Siyasa wanda kullum shi a yabon kansa yake shi kadai tsabar son rai?

To bara ku ji na fada muku, idan kun hana a fada masa gaskiya a nan gidan duniya, to ku sani baku isa ku hana Allah ya yi masa hissabi ba bisa ga yadda ya gudanar da mulkinsa da kuma rayuwarsa ba ranar gobe.

Saboda haka a yi hattara dan Allah, Siyasa ba hauka bane.

TUNATARWA

TUNATARWA

'Yan Uwa Musulmi Kada A Manta Da Daren Daren 'Lailatu Qadri'

ABUBUWA 15 DA ALLAH YA FIFITA DAREN LAILATUL QADRI AKAN DUKKAN DARARE BAKI DAYA

Daga Aliyu Ahmad

*1-Allah ya zabi wannan dare na lailatul Qadri, ya fifita shi ya daukaka shi cikin falala da daraja da daukaka akan dukkan sauran darare baki daya*

*2-Sanyawa wata sura daga cikin surorin Alqurani mai girma SURATUL QADRI* (Dan girmama sha'anin wannan Dare.

*3-Allah ya girmama sha'anin wannan dare na Lailatul Qadri*

*4-Daren lailatul Qadri dare ne mai albarka mai yawa*

*5-A cikin Daren lailatul Qadri ne Allah ya saukar da Alqurani zuwa saman Duniya a baitul Izza*

*6-Aiyukan ibada a wannan dare ya fi alkairi da matsayi da falala akan dararen watannin dubu wanda babu daren lailatul Qadri*

*7-Wanda ya dace da wannan dare kuma ya yi ibada a cikinsa, ya sami alkairi mai yawa, wanda kuma ya yi asarar wannan dare, to an haramta masa alkairi mai yawa*

*8-Wanda ya raya daren da ibada yana mai imani da kwadayin samun lada,to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa*

*9-Raya darare goma na karshen Ramadan dan dacewa da Daren Lailatul Qadri, yin hakan sunna ce ta Manzon Allah s.a.w*

*10-Manzon Allah S.A.W ya koyar da yin wannan addu'ar a cikin wannan dare don samun afuwa da gafarar Allah"
*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ*

*11-Mala'iku masu yawa har ma da Shugaban Mala'iku wato Mala'ika Jibrilu suna saukowa cikin wannan dare*

Suna saukowa ne domin yin addu'a da nemawa bayin Allah da suke raya wannan dare da ibada gafara a wajen Allah.

*12-Daren mai aminci da walwala tun daga faduwar rana har zuwa fitowar Alfijir*

*13-A cikin wannan dare ne Allah yake tsarawa da rubuta Arziki da Ajali da sauran al'amurar wannan shekara gaba daya*

*14-Shaidan da rundunarsa ba su iya fitowa dan yada alfasha ga dan Adam a cikin wannan dare*

*15-Nemn Daren Lailatun Qadri da kirdadonsa yana cikin shiriyar Annabi s.a.w*

  Allah ne mafi sani.

*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ

GIYA DA SIGARI ZASUYI TASHIN GORON ZABO A NAJERIYA

GIYA DA SIGARI ZASUYI TASHIN GORON ZABO A NAJERIYA.

A yau akesa ran sabon harajin kudin giya dana taba zai fara aiki a Najeriya,  wata majiya mai tushe  tace ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan sabon tsarin harajin a yau kuma yafara aiki cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A karkashin sabon harajin, Tabar sigari, za'a ma ta karin kashi 20 cikin dari na haraji, yayinda duk karan sigari daya zata samu karin naira 1 a shekarar 2018,  a shekarar 2019 karin haraji zai koma Naira 2 akan duk kara daya, a shekarar 2020 kuma karin harajin zai tashi zuwa Naira 2.90 a duk kara daya.

Shi kuma sabon tsarin harajin giya zai shafi Beer, stout, wines da spirits na shekara 3, daga 2018 zuwa 2020.

Ministan kudi, Misis Kemi Adeosun, tace sabon tsarin harajin giya dana taba sigarin wani matakine  na gwamnati domin rage matsalolin rashin lafiya da ke tattare da taba da giya.

Annobar Amai Da Gudawa Ta Barke A Nasarawa

Annobar Amai Da Gudawa Ta Barke A Nasarawa
___¥__
*
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun nuna cewa annobar Amai da Gudawa ta barke a yankin Angwan Lambu da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.

A halin yanzu dai, annobar ta yi sanadiyyar mutuwar wata mata yayin da wasu mutane 20 suka kamu da annobar wanda ya hada har da wasu daliban jami'ar Nasarawa da ke Keffi. Da yake tabbatar da barkewar annobar, Kakakin Jami'ar, Abraham Ekpo ya ce, ana duba daliban da annobar  ta harba a karamin asibitin jami'ar.

Wasu Mahara Sun Kai Hari Gidan Kurkukun Minna

Wasu Mahara Sun Kai Hari Gidan Kurkukun Minna
___¥___
*
Wasu mahara sun kai wani mummunan hari a gidan kurkukun garin Minna da ke jihar Neja inda suka kashe wani jami'in hukumar kula da gidajen kurkuku tare kuma da arcewa da wasu fursunoni guda biyu.

Kakakin Gidan Kurkukun, Rabi'u Shuaibu ya ce, miyagun sun kai harin ne a daren jiya Lahadi inda suka yi musayar harbe harbe da masu tsaron gidan kurkukun wanda a sakamakon haka suka harbe wani dan Achaba wanda ya kawo wani jami'in gidan kurkukun.

YA KAMATA A DAKATA HAKA NAN


YA KAMATA A DAKATA HAKA NAN

DALILI NA ....

Daga Shehu ladan Army Malumfashi

Watau abin da yasa na bada HAKURI na kuma ce a saurara a kauda kai shi ne, Ina gudun kar rikicin cikin gida ya cinyemu, idan nace cikin gida ina nufin,Musulmai da Arewa da Hausawa da kuri 'unmu.

Sanin kowane abokan zaman mu a Nigeria ba su zabi BUHARI ba a 2015, kuma duk da dumbin ayyukan raya kasa da ya ke tayi masu, karfa ku dauka cewa wai za su zabe shi a 2019.

Mu dai ne muka zabi abin mu da kanmu, kuma mu ne za mu kara zabar shi dai a 2019,To ku daina mugayen kalamai a kan wadanda su ke tare da jama'a, kuma jama'a suke goyon bayansu ko da mabiyansu yan kadanne, domin wadannan kalaman na ku za su iya jawo tsananin kiyayya ga wanda ku ke karewa har tana iya kai ga rasa kuri'ar almajiransu ko mabiyansu.

Misali kun ga akwai gaba da kiyayya da ke ta yaduwa
tsakanin BUHARAWA da ATIKAWA da KWANKWASAWA da TINUBAWA da SHI 'AWA da wasu SANATAWA da wasu WAKILAWA, wannan kowa ya sani, to yanzu kuma za ku cigaba da rura wata sabuwar adawar.

Ku sani duk wadannan kalubale ne a siyasance wanda WALLAHi sun fi karfin a raina su, saboda duk wannan wutar tana ruruwa ne a wuraren da ake sa ran samun
kuri'u masu yawa.

Kuma ku masu kausasa Kalman nan ba ku iya
kawo su, idan aka kwatanta da mabiyan wadanda na ayyana a sama, domin su mabiyan suna jin maganar su, Kar mu dabawa cikinmu wuka.

SHAWARA: Ku zubar da makaman nan haka nan, siyasa ba ta son fada da masu magoya baya da yawa, kuma idan aka maida martani sai a saurara, amma wasu sai cillo makamai masu linzami su ke yi ba kakkautawa,kun ga yanzu wadancan fa dadi za sui ta ji, domin yakin da ya kamata su yi da kansu ne mu ke yi masu, kuma dai kun san zabe yana gab da kurewa ko? Sannan ku kyale shi da yan'uwanshi malamai ku ji ta inda za su bullo ma shi, kamar yadda shi ma BUHARIN ai kun ji yadda yan siyasa su ka yi ma shi dangane da kalaman shi na baya.

To kowace kwarya da abokiyar burminta, Shi
dan siyasa na sosai kullum haduwa ya ke so ba rabuwa ba.

Allah ya kara had'a kawunnan mu Ameen.