spon

Sunday, September 2, 2018

YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
 TITTLE YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI.
KAYAN HADI*
  • Kwai
  • Kifi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Fulawa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyada
 
*YADDA ZA KIYI*
Da farko ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki ďora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cicire 'kayar shi sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, ki fasa 'kwai kaďan ki zuba a ciki, ki ďauko fulawa ki zuba(hikimar sa fulawa dan ya haďe jiki ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe
 
SPINACH EGG SAUCE

INGREDIENTS:
1. Spinach (Alayyaho)
2. Eggs, oil
3. Tattasai, tarugu, albasa and garlic.
 
PROCEDURE: A wanke alayyaho a yayyanka qanana, sai a yayyanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko zaki samu tukunyar da babu komai a wuta ki juye alayyahon duka ki ďan turara sa. In kina da steamer zaki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.
Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in ya ďan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu ki juye alayyahon ki jujjuya su hade.
Ki kaďa eggs ki juye a ciki ki juya su haďe da kyau, in ya gama soyuwa sai ki sauke. Zaki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma doya da dankali.
Note: Zaki iya zuba isashen kwai ni nafi son shi a haka. Ba dole sai spinach ba zaki iya yi da sauran ganyayyaki. Kuma zaki iya yi babu kayan miya, idan kika yi steaming alayyahon tare da albasa sai ki kaďa kwai ki juye a ciki. A kula sosai idan kin yanka alayyaho ne kafin ki yanka to ki zuba ruwa isashe yanda zai taso sama sai ki kwashe zaki ga qasan ya koma qasa in ba haka ba zaki rinqa ci kina jin qasa. Yana da dadi in aka sanya a shinkafa. Ga kuma qara lfy.
 
Gashashen Kifi/ Grilled Fish
Kayan Hadi:
1. Kiyin Karfasa / Tilapia
2. Albasa, lemun Tsami, Citta, Kanunfari, Masoro, Tafarnuwa, Garin Yaji ko Tarugu.
3. Maggin Knorr, Gishiri, Kori, Thyme, da kayan Qamshi da Dandano
4. Myan Gyada.
Yadda Zaki Sarrafa: Ki wanke kifin ki ciki da bai, saka hannu har cikin bakin kifin ki wanke shi sosai. Bayan kin wanke sai ki tsane ruwan in sauri kike yi kisa towel ko tissue ki cire ruwan.
Daga nan sai ki daka ko kiyi blending kanunfari da masoro, citta, thyme, da sauran su. In kuma kina da garin su shikenan. Sai ki juye a mixing bowl.
Sannan ki dauko albasa kamar rabi haka ki saka, ki zuba tafarnuwa biyu manya, idan ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi blending ko daka yayi luqui luqui. Haka nan in tarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi.
Daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba curry kadan, ki zuba knorr da gishiri, sannan ki matse lemun tsami qaramin cokali daya ki zuba. Sai ki zuba oil yanda hadin zai kama jikin kifin.
Bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki. Sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a fridge yayi kamar minti 30 in a freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi qanqara ba.
Daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da oven ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin ki, kina yi kina jujjuya wa har ya gazu.
Hadin Sauce/Sauce
Kayan Hadi:
1. Albasa biyu ko uku
2. Tarugu, Tattasai da Green pepper
3. Tafarnuwa 1
4. Gishiri da Maggi knorr
Yadda Zaki Hada Sauce: Farko zaki yanka albasanki da tattasai da green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura mai a tukunya kamar quater qaramin ludayi, in yayi zafi ki zuba albasan da tattasan, ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba niqaqqen tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa tare da sinadarai, sai ki dan zuba ruwa kadan yanda zasu dahu. Zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida.
Daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din a sama. Ai haka zaki ji kawai yana shigewa cikin tumbin maigida yana santi.
Kada a manta a ajiye wa mai gida lemun tsami na wanke hannu bayan ya gama ci saboda qarni. Sannan a tabbata an saka ginger ko citta, tafarnuwa da kanunfari don suna da muhimmanci a gashi.

YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
      TITTLE:YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

Abubuwan hadawa

  • Semonvita kofi 1/2
  • Madara cokali 6
  • Suga dai dai dan dano

Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tukunyarki, ki sa ruwa ki dora a wuta ya tafasa.
  2. Sai ki dauko semonki ki dama da ruwa ya yi kamar za kiyi talge.
  3. Sai ki duba idan ya tafasa sai ki zuba a kan ruwan ki juyashi sosai.
  4. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba a kwano ki sa madara da suga sai ki juya ki zubawa kowa a kofi.

A sha dadi lafiya. Na gode sai mun hadu girki n a gaba.

Ba na tsoron fafatawa a zabe na gaskiya — Buhari

HOME/POST FILE UNDER LABARAI
AUTHOR:AREWAINFINIT
DATE:SUN SEP 2 2018
 
NIGERIA PRESIDENCY
Image captionGwamnan jihar Lagos, wanda ake rade-radin cewa zai fice daga APC, na cikin tawagar Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba ya tsoron fafatawa a zabe idan za a gudanar da shi cikin gaskiya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar China a birnin Beijing inda yake ziyara.
A cewar sa, "Ba na jin tsoron karawa a zaben da za a gudanar cikin gaskiya saboda shi ne ya sa na zama shugaban kasa. Na san irin faman da na yi inda sau uku ina tsayawa takara ina faduwa zabe amma ina kalubalantar sakamakon sa a kotun koli."
"Da na fadi a zabe karo na uku na ce 'Allah ya saka min'; daga bisani aka yi amfani da fasahar na'ura wuririn gudanar da zabe kuma hakan ya taimaka mana,' in ji Shugaba Buhari.

President Muhammadu Buhari, has named a new management for the Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC.

HOME/post file under breaking news
Author:Arewainfinit.con
  President Muhammadu Buhari, has named a new management for the Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC.

Those appointed include: Abbas Masanawa as Managing Director, and Abubakar Minjibir, Chris Orewa, and Tunji Kazeem, as Executive Directors.

(Wasu mutane 'ba sa so a daina zub da jini a Nigeria')

HOME/post file Under labarai/
Author /Arewainfinit/
Post Tittle:wasu mutane basa so a daina zubda jini a Nigeria.
Ministan tsaron Najeriya ya ce wasu kungiyoyin kasashen waje ba sa so a daina rikice-rikice a kasar.
Mansur Dan-Ali ya shaida wa cealkaluman da wasu kungiyoyin kasar waje ke fitar kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya ba gaskiya ba ne.
Yana yin raddi ne game da rahoton da kungiyar da ke bincike a kan rikice-rikice ta International Crisis Group ta fitar kwanakin baya cewa rikicin manoma da makiyaya da ya faru a jihohin Benue, Filato, Adamawa, Nassarawa da kuma Taraba ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 1300 tun daga watan Janairun 2018.
Kungiyar ta ce wadannan alkaluman sun nunka na mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a wannan shekarar sau shida.Abin da mutane ba su gane ba shi ne [kungiyoyin nan] suna da tasu manufa, idan ka ga abubuwan da suke yi a Maiduguri, suna so su karfafa rikicin ya kara yawa ne, wadansu daga cikinsu ba sa son ya kare saboda a nan suke samun kudinsu," in ji ministan.
Sai dai babu wata shaida da BBC ta samu da ta gaskata wannan zargi.
Ministan ya kara da cewa bai san adadin sojojin kasar da aka kashe a rikice-rikicen da aka yi cikin wata uku ba.
Sai dai ya ce gwamnatinsu tana daukar matakai na shawo kan matsalolin tabarbarewar tsaro da ke faruwa a Najeriya.

VIDEO] DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 69

HOME/Dadin kowa/


VIDEO] DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 69

Author/Arewainfinit/ Date Sun 2sep 2018
Domin Kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya wuce kawai ku biyomu.
Acikin Wannan Satin:
Stephanie za ta ziyarci Nasir a gida don duba lafiyarsa, inda zata hadu ta Malam Hassan.
Yaya a zata kasance tsakaninsu? Malam Hassan zai amince da alakarta da Nasir?
Stella za ta zo Dadin Kowa don daukar Wizzy zuwa garin.
Shin Wizzy zai amince ya bi Stella kuwa?
Duk Acikin Wannan Satin.
WNLOAD VIDIO HEREVIDMATEVIDMATE/DOWNLOAD/HERE