spon

Showing posts with label labarai. Show all posts

Monday, June 4, 2018

RA'AYI: Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba

Daga Zee Taraba

Dan Allah masu yi wa Buhari makauniyar soyayya ida kun isa ku hana Allah ya yi masa hisabi ranar gobe tunda ku ba za ku fada masa gaskiya ba kuma ba za ku bari masu tsoron Allah su fada masa gaskiya ba.

Mun lura abun naku ya soma wuce gona da iri, har ta kai ga kuna zagin Malaman addini akan siyasar banza wadda kwata-kwata duk rantsi duk jimawa shekaru takwas kacal ake akan kujerar.

Mulkin Buhari babu hali Malami ya ce zai fito ya fadawa Buhari gaskiya sai a soma cewa wai malamin siyasa ne, idan kuma ya yaba Buhari sai a ce na addini ne tsabar son zuciya irin namu.

Wai shi Buhari yafi karfi a fada masa gaskiya ne?

A ce wai Malaman addini a ringa zagin su akan wani dan Siyasa wanda kullum shi a yabon kansa yake shi kadai tsabar son rai?

To bara ku ji na fada muku, idan kun hana a fada masa gaskiya a nan gidan duniya, to ku sani baku isa ku hana Allah ya yi masa hissabi ba bisa ga yadda ya gudanar da mulkinsa da kuma rayuwarsa ba ranar gobe.

Saboda haka a yi hattara dan Allah, Siyasa ba hauka bane.

Annobar Amai Da Gudawa Ta Barke A Nasarawa

___¥__
*
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun nuna cewa annobar Amai da Gudawa ta barke a yankin Angwan Lambu da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.

A halin yanzu dai, annobar ta yi sanadiyyar mutuwar wata mata yayin da wasu mutane 20 suka kamu da annobar wanda ya hada har da wasu daliban jami'ar Nasarawa da ke Keffi. Da yake tabbatar da barkewar annobar, Kakakin Jami'ar, Abraham Ekpo ya ce, ana duba daliban da annobar  ta harba a karamin asibitin jami'ar.

YA KAMATA A DAKATA HAKA NAN

YA KAMATA A DAKATA HAKA NAN

DALILI NA ....

Daga Shehu ladan Army Malumfashi

Watau abin da yasa na bada HAKURI na kuma ce a saurara a kauda kai shi ne, Ina gudun kar rikicin cikin gida ya cinyemu, idan nace cikin gida ina nufin,Musulmai da Arewa da Hausawa da kuri 'unmu.

Sanin kowane abokan zaman mu a Nigeria ba su zabi BUHARI ba a 2015, kuma duk da dumbin ayyukan raya kasa da ya ke tayi masu, karfa ku dauka cewa wai za su zabe shi a 2019.

Mu dai ne muka zabi abin mu da kanmu, kuma mu ne za mu kara zabar shi dai a 2019,To ku daina mugayen kalamai a kan wadanda su ke tare da jama'a, kuma jama'a suke goyon bayansu ko da mabiyansu yan kadanne, domin wadannan kalaman na ku za su iya jawo tsananin kiyayya ga wanda ku ke karewa har tana iya kai ga rasa kuri'ar almajiransu ko mabiyansu.

Misali kun ga akwai gaba da kiyayya da ke ta yaduwa
tsakanin BUHARAWA da ATIKAWA da KWANKWASAWA da TINUBAWA da SHI 'AWA da wasu SANATAWA da wasu WAKILAWA, wannan kowa ya sani, to yanzu kuma za ku cigaba da rura wata sabuwar adawar.

Ku sani duk wadannan kalubale ne a siyasance wanda WALLAHi sun fi karfin a raina su, saboda duk wannan wutar tana ruruwa ne a wuraren da ake sa ran samun
kuri'u masu yawa.

Kuma ku masu kausasa Kalman nan ba ku iya
kawo su, idan aka kwatanta da mabiyan wadanda na ayyana a sama, domin su mabiyan suna jin maganar su, Kar mu dabawa cikinmu wuka.

SHAWARA: Ku zubar da makaman nan haka nan, siyasa ba ta son fada da masu magoya baya da yawa, kuma idan aka maida martani sai a saurara, amma wasu sai cillo makamai masu linzami su ke yi ba kakkautawa,kun ga yanzu wadancan fa dadi za sui ta ji, domin yakin da ya kamata su yi da kansu ne mu ke yi masu, kuma dai kun san zabe yana gab da kurewa ko? Sannan ku kyale shi da yan'uwanshi malamai ku ji ta inda za su bullo ma shi, kamar yadda shi ma BUHARIN ai kun ji yadda yan siyasa su ka yi ma shi dangane da kalaman shi na baya.

To kowace kwarya da abokiyar burminta, Shi
dan siyasa na sosai kullum haduwa ya ke so ba rabuwa ba.

Allah ya kara had'a kawunnan mu Ameen.

Sunday, June 3, 2018

Mun kusa hadewa da wasu jam'iyyun adawa don fatattakar APC a 2019 - PDP

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Prince Uche Secondus ya shaidawa wakilin kamfanin jaridar Punch cewa tuni shirye-shiryen hadewa da sauran jam'iyyun adawa a kasar nan domin kawar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019 yayi nisa.

Shugaba Secondus ya bayyana cewa kwamitin da jam'iyyar ta kafa karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas na samun gagarumar nasara don kuwa tuni sun kai wani mataki na fahimtar juna da wasu jam'iyyun.

Mun kusa hadewa da wasu jam'iyyun adawa don fatattakar APC a 2019 - PDPKU KARANTA:An mallakawa Yarima Bin Salman ikon Makka da Madina

Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su

A yau ne hukumar ‘yan sanda ta aike da takardar gayyata ga shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, bayan wasu gungun ‘yan fashi da aka kama sun bayyana cewar Saraki na daga cikin mutanen da suke yiwa ayyukan ta’addanci.

Hukumar ta ‘yan sanda tace yanzu haka tana tsare da mutane 22 da take zargi da hannu cikin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu tare da kashe mutane kimanin mutumin 33.

Ga jerin sunayen mutanen da inda suka fito kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta wallafa

Sugabannin gungun 'yan fashin shine:
1. Ayoade Akinnibosun,mai shekaru 37 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.

2. Ibukunle Ogunleye, shekaru 36 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

3. Adeola Abraham, shekaru 35 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 5

4. Salawudeen Azeez, shekaru 49 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

5. Niyi Ogundiran, shekaru 37 –daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.
Ya kashe mutane 2

6. Michael Adikwu,shekaru 30 – Ya kashe mutane 22, yawancin su 'yan sanda.

7. Kabiru Afolabi, shekaru 26

8. Omoseni Kassim, shekaru 28

9. Kayode Opadokun, shekaru 35

10. Kazeem Abdulrasheed, shekaru 36

11. Azeez Abdullahi, shekaru’ 27

12. Adewale Popoola, shekaru 22

13. Adetoyese Muftau, shekaru 23

14. Alexander Reuben, shekaru 39

15. Richard Buba Terry, shekaru 23

16. Peter Jasper Kuunfa, shekaru 23

17. Ikechukwu Ebuka Nnaji shekaru 29

18. Moses Godwin, shekaru 28

19. Adeola omiyale, shekaru 38, daga garin Isanlu Isin, Isin LGA, Kwara State.

20. Femi Idowu, shekaru 34

21. Alabi Olalekan, shekaru 49-mai taimakawa gwamnan jihar Kwara na musamman

22. Yusuf Abdulwahab, shekaru 58 –Shugaban ma'aikatan jihar Kwara.

Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda ya kama Saraki

A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi masa da zarar takardar gayyatar ta same shi.

Kazalika, Saraki ya musanta cewar akwai wata alaka dake tsakanin sa da mutanen da ake zargi da aikata laifin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.

A yau, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu daga cikin wadanda ta kama dangane da batun fashin bankunan garin Offa sun ambaci sunan Saraki da na gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a matsayin mutanen dake daukar nauyin aiyukan su na ta’addanci.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya , Ibrahim K. Idris, ya kama Saraki bayan gabatar masa da shaidar samun hannun Saraki a cikin aiyukan ta’addanci, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Zuwa yanzu Kakakin shugaban kasa da na hukumar ‘yan sanda sun ki cewa komai a kan wannan batu dama kuma batun ganawar shugaba Buhari da shugaban na ‘yan sanda ta ranar juma’a.

Da yake jawabi cikin sanarwar da mai Magana da yawun sa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar, Saraki yace alakanta shi da fashi wani makirci ne kawai na bata masa suna.

An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

A jiya Juma'a ne dai wasu 'yan bindiga suka kashe Mutane har 23 a jihar Zamfara a kauyen Zanoka bayan da suka budewa mazauna kauyen wuta kan mai Uwa da wabi sannan kuma suka cinnawa Gidajen Mutane wuta suka kone kurmus.

Barayin dai sun zo ne kan Babura a matsayin daukar fansar korar da 'yan sintirin yankin su kayi musu inji shugaban karamar hukumar yankin da abin ya faru Mustapha

"Yanzu haka mun binne mutane 23 ciki har da 'yan sintiri da su kayi kokarin dakatar da su."

Mustapha Muhammad ya bayyana cewa 'yan Bindigar sun fara kai farmakin ne ranar Juma'a inda har suka kwacewa Mutane shanunsu sai dai jami'an sintiri na yankin sun fatattake su sannan suka kwato shanun, a dole suka tafi.

Amma sai dai 'yan awanni kadan bayan faruwar hakan sai Barayin suka sake dawowa da babbar runduna kauyen dake nisan Kilomita 160 daga babban birnin Gusau

Kakakin rundunar 'Yan sanda na jihar ta Zamfara Muhammad Shehu ya shaida cewa sun samu gawawwaki 15 bayan da 'yan Bindigar suka kai harin.

"Mafi yawan wadanda suka Mutun 'yan sintiri ne na yankin da su kayi kokarin dakatar da su."

Barayin sun sha kai hare-hare domin sace shanun Mutane tsawon shekaru da dama su kuma kashe duk wani wanda ya nuna tirjiya ga abinda suka aikata.

Wadannan har-hare da ake kai musu ya sanya 'yan Kauyen suka kafa kungiyoyin 'yan sintiri domin tabbatar da tsaro a yankin, amma sai dai su kansu 'yan sintirin ana zarginsu da cin zarafi da kashe wadanda suka kama bisa zargin su.

Yawaitar aiyukan tsagerun ma ya sanya Gwamnati ta kai rundunonin tsaro jihar domin tabbatar da dawo da doka da oda, amma sai dai har yanzu lamarin na dada kamari.

Hotunan yadda Aisha Buhari ta yi buda baki da shugabannin Mata

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa.
Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa a ranar Asabar
Buda bakin ya samu halartar mata daga kungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida da kungiyoyin addinai da sauransu.
Daga cikin wadanda aka gayyata buda bakin har da BBC, kuma Raliya Zubairu da Fatima Othman ne suka wakilci BBC
A wajen buda bakin, Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari da uwar gidan mataimakin shugaban kasa sun gabatar da jawabi

Tsakanin Gwamna Taraba Da Maman Taraba : Ina masu fada saboda yan siyasa? Yanzu mun hankalta?

Lokacin da maman Taraba Hajiya Jummai Alhassan ke neman kujerar gwamnan Taraba da ita da Gwamna mai ci Darius Ishaku abin ya tashi daga APC da PDP inda abin ya koma na addini.

Daga baya daya kayar da ta sai Buhari ya bata Minista.
Shi yana gwamna ita Minista duka suna samun kudade.

Bayan shekaru kadan sai tace Atiku ne mai gidan ta kuma ko ina zata iya bin shi ta kyale Buhari.

Yau gashi gwamnan Taraba da Maman Taraba suna rike da hannun juna.

Ina magoya bayan nasu daga yan APC da PDP, musulman da kiristocin?
Na tabbata da yawan su na nan babu aikin yi.

Wednesday, March 14, 2018

GEN:MUHAMMAD BUHARI YANA MAGANA AKAN NPOWER

Domin cewa duk Wanda ya cike npower domin Neman aiki zai samu Dan Allah akara hakuri za a fara April domin daukar mutane aiki Amman Dan Allah a da dahakuri jama a akan alkawarin da akai muku sai munhadu a April

Saturday, February 17, 2018

Obasanjo ya kai wa Jonathan ziyara

Cif Obasanjo ya sha caccakar Mr Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ziyara a gidansa da ke Otueke da ke kudu maso kudancin kasar.
Cif Obasanjo ya je jihar Bayelsa ne domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta yi, a cewar jam'iyyar PDP da ke hamayya a kasar.
"Daga nan ne ya kai ziyara wurin Goodluck Jonathan a gidansa da ke Otuoke," in ji PDP, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Mr Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka tarbi tsohon shugaban kasar.
A baya dai, Obasajo ya soki Mr Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki a lokacin da yake shugabancin Najeriya, yana mai cewa Obasajo dai ya soki shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki, yana mai cewa Mr Jonathan na so ya sake cin zaben kasar ko ana so ko ba a so idan ba haka ba kuwa zai jefa kasar cikin rikici.

Cif Obasanjo ya zama shugaban Najeriya sau biyu, kuma shi ne ya zabi shugaba Jonathan domin zama mataimakin marigayi shugaba Umaru 'Yar Adua.
A watan jiya, Cif Obasanjo ya soki Shugaba Buhari saboda "rashin iya shugabanci" inda ya yi kira a gare shi da kada ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar.
Ya kafa wata kungiyar siyasa da ya ce ita ce za ta iya ceto kasar daga kangin da take ciki.
Masu sharhi na gani tsohon shugaban gwano ne da ba ya jin warin jikinsa, suna masu cewa shi kansa bai iya mulki ba lokacin da ya yi shugabancin kasar.

Wednesday, January 24, 2018

Me 'yan Nigeria ke cewa kan wasikar Obasanjo ga Buhari?

Muhawara ta barke tsakanin 'yan Najeeriya kan wasikar da Obasanjo ya rubutawa Buhari
Wasikar da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar a ranar Litinin inda yake bai wa Shugaba Buhari shawara cewa kar ya sake yin tazarce a 2019 ta jawo muhawara mai zafi a tsakanin 'yan kasar.
Muhawarar ta barke a shafukan sada zaumunta da ma kafafen watsa labarai daban-daban inda mutane ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.
A cikin bwasikar wacce Obasanjo ya aikewa manema labarai, ya caccaki Shugaba Buhari da cewa kamata ya yi ya bar mulki a 2019 ya je ya huta saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa.
Ya kuma fiddo da wasu abubuwa da ya kira nakasu da kasar ke fuskanta wadanda a dalilinsu ne a zaben 2015 mutane suka fita kwai da kwarkwata don zabar Buhari da yakinin cewa shi ne zai magance musu wadannan matsaloli, "amma sai ga shi ba ta sauya zani ba," in ji tsohon shugaban kasar.
A baya dai

A shafukan Twitter da Facebook dai mutane sun ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke ganin lallai maganganun Obasanjo gaskiya ne kuma a kan hanya suke.
JJ Omojuwa wani fitaccen mai amfani da shafin twitter ne ya kuma rubuta cewa: "Argh! Lallai wannan alama ce da ke nuna cewa 2019 ta sako kai. Obasanjo bai taba fadar magana irin wannan a kan shugaban kasa kafin zabe ba kuma ba ta faru ba. Ga 'yan kallo irin ku da dama, za ku iya cewa lallai wannan ce shimfida ta abun da zai faru a zaben 2019."
Wasu kuwa cewa suke lallai Mista Obasanjo bai taba faduwa wani zabe da shi ya tsaya takara ko ya marawa wani baya ba tun daga shekarar 1999 da 2003 da 2007 da 2011 da kuma 2015.
Da zabukan da ya tsaya karkashin PDP guda hudu, da wanda ya marawa APC baya guda daya, a yanzu kuma ga shi ya nuna alkiblarsa ba tare da marawa ko wacce jam'iyya baya ba. Ko me zai faru?
Ita ma Nedu Okeke wacce take shafin Twitter da sunan @Nedunaija got=yon bayan wasikar ta yi da cewa: "Obasanjon da ya mara maka baya a 2015 ma ya ba ka shawara da cewa kar ka sake tsayawa takara saboda gazawarka.
"Matarka da ta goyi bayanka a 2015 ma ta nuna alamar cewa ba za ta sake goyon bayanka ba. Baba, don Allah ka tafi gida
Kazalika a hannun guda kuma akwai dumbin mutanen da suke sukar Obasanjo kan wannan wasika da ya aike wa Buhari.
@abubakar471 ya rubuta cewa: "Idan har obasano zai tsayar mana da 'yan takara sau uku, kuma dukkansu ba shugabanni na-gari ba ne, to don me ya sa zan gaskata son ransa a yanzu?"
Wani kuwa mai suna Parodidant Buhari a Twitter ya rubuta cewa: "Ga dukkan alamu Obasanjo bai san cewa bai yi tsufa da shiga gidan yari ba."

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a nata martanin cewa ta yi: Tsohon shugaban Najeriya ya tabbatar da matsayin da muka dade a kansa cewa gwamnatin Buhari da APC sun gaza a ko wanne fanni.
"Sai dai muna kira ga mutane da kar su yarda da kirkiro wata sabuwar kungiyar siyasa kamar yadda ake ta kira, maimakon haka gara su marawa PDP baya don ta ceto su."
Shi kuwa shugaban jam'iyyar APGA Dr. Victor Oye, cewa ya yi "Dr. Obasanjo bai cancanci shawartar Buhari kar ya sake tsayawa takara ba, kuma ya daina jawo tayar da hakarkari ba gaira ba dalili."
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Obasanjo ya taba aikewa wani shugaban kasa wasika cewa kar ya yi tazarce ba, a baya ma ya taba aikewa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan wasika cewa kar ya yi ta-zarce a 2015.
Wannan batu dai zai ci gaba da jan hankalin 'yan Najeriya a ciki da wajen kasar, sai dai babu tabbas ko wannan kira na Obasanjo zai yi tasiri ko ba zai yi ba, musamman ganin cewa wannan shekara ta 2018 ita ce wacce za a bambance tsakanin aya da tsakuwa kafin zaben 2019.

2019: 'Batun tazarce ba shi ne a gaban Buhari ba'

  1. Ministan ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce maganar sake tsayawa takara ba shi ne a gaban Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba a wani martani da ya yi ga tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.
  1. Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa BBC ranar Laraba.
    A ranar Talata ne Mista Obasanjo ya rubuta wata budaddiyar wasika wadda ya ba Shugaba Buhari shawara kan kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
    Jami'in gwamnatin ya ce wajibi ne a yaba wa Buhari kan abubuwa biyu cikin ukun da aka yi kamfe a kansu; wato yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu tada kayar-baya.
    Har ila yau, ministan ya ce tsohon shugaban ya ce gwamnatin Buhari ba ta samu nasara ba a fannin tattalin arziki saboda shi ne na uku cikin jerin alkawurran da aka yayin kamfe.
    Daga nan ya ce yana ganin cewa aikace-aikacen Obasanjo ne ba su "ba shi sukunin fahimtar dimbin ayyukan ci gaban da gwamnatin Buhari take gudanarwa ba a halin yanzu musamman a fannin bunkasa tattalin arziki."
    Ministan ya kuma ce dukkan alkalumman da ake amfani da su wajen bayyana karfin tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya na samun ci gaba.
    Hakazalika ya ce kasar ta fita daga matsin tattalin arziki ne ta hanyar amfani da shawarwarin da wadansu 'yan kasar suke ba ta.
    Bugu da kari, ministan ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere.
    Ya ce fito tsarin amfani da asusu na bai daya wato (TSA) ya sa gwamnatinsu ta tara naira biliyan 108 kuma ya ce kasar tana adana fiye da naira biliyan 24 a kowane wata daga sabon tsarin.
    Jami'in gwamnatin ya ce sun samu naira biliyan 120 bayan sallamar ma'aikatan bogi. Haka dai ministan ya yi ta zayyana nasarorin da gwamnatin ta samu daya bayan daya a cikin sanarwar.
  2. Kan batun rikicin manoma da makiyaya ya ce gwamnatinsu a shirye take ta kawo karshen matsalar duk da cewa gadon matasar suka yi daga gwamnatin da ta gabace su, kamar yadda ya ce.
    Daga nan ya bukaci 'yan kasar da su ba su goyon baya don ganin an magance hakan.
    Game da batun tazarcen shugaban kuwa, ministan ya ce da gaske na wadansu 'yan kasar suna kiraye-kirayen neman ya sake tsayawa takara, yayin da wadansu kuma suke nuna adawarsu ga hakan.
    "Muna ganin wannan batun zai iya raba hankalin shugaban a halin yanzu saboda ya dukufa a kowace sa'a don ganin ya magance dimbin matsalolin da suke ci-wa kasar tuwo a karya wadanda galibinsu gadonsu ya yi daga tsoffin gwamnatocin da suka gabata," in ji shi.
    Har ila yau ya ce ba su taba tunanin cewa tsohon Shugaba Obasanjo yana da wata manufa ba kan wasikar bayan ci gaban kasa.
    "Mun karbi shawarwarinsa da zuciya daya kuma muna gode masa kan yadda ya samu lokaci duk da dimbin aikace-aikacen da ke gabansa ya rubuta mana wannan doguwar wasikar," in ji ministan.
    Ita ma jam'iyyar APC a martaninta yaba wa tsohon shugaban ta yi.
    Sai dai ta ce ba duka abubuwan da ya fadi ba ne a wasika ta yarda da su, musamman game da jam'iyyar da kuma gwamnatin Najeriya.
    Sakataren yada labaran jam'iyyar Malam Bolaji Abdullahi ya ce "ba gaskiya ba ne yadda tsohon shugaban ya yi watsi da tsarin jam'iyyun kasar duka.

Saturday, January 20, 2018

Nigeria: An kubutar da turawan da aka sace a Kaduna

An baza jami'an tsaro masu yawan domin neman turawan da aka sace a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce an samu nasarar kubutar da turawan nan hudu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a makon jiya.
An sace mutanen hudu ne da suka hada da Amurkawa biyu da 'yan kasar Canada biyu a lokacin da suke aikin samar da hasken lantarki ta hanyar amfani da hasken rana a Najeriya.
A ranar Talatar da ta gabata ne aka sace turawan a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa Abuja daga Kaduna.
An shiga neman turawan ne gadan-dagan jim kadan bayan sace su, inda aka tura jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma wani jirgi mai saukar ungulu cikin daji domin neman turawan.
Kwamishinan 'yan sanda ta jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, an kubutar da turawan ne a wani daji bayan da wadanda suka sace su suka gudu suka bar su a wajen, amma kuma an yi nasarar kama daya daga wadanda ake zargi da sace turawan
Yanzu haka dai an duba lafiyar turawan.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka yi wa jerin gwanon motocin turawan kwantan bauna a wani daji dake da nisan kilomita 200 daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an kashe 'yan sandan Najeriya biyu da ke bawa turawan kariya a lokacin satar turawan .
Satar mutane don neman kudin fansa na dada kamari a Najeriya, a dai-dai lokacin da kasar ke fama da rikicin Boko Haram da matsin tattalin arziki mafi tsanani a shekaru da dama.
Kuma Jihar Kaduna na daga cikin sassan kasar da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa.
Ko a watan Fabrairun bara an taba sace wasu Jamusawa guda biyu, kafin daga bisani aka sake su. Haka ma a watan Oktoban da ya gabata an sace wasu Turawan Birtaniya a yankin Neja Delta inda aka saki uku, bayan an kashe daya daga cikinsu.

Sunday, January 7, 2018

Sabon rikici ya barke a Taraba

Al'amarin ya faru ne a karamar hukumar Lau, da Katibu da kuma sauran kauyukan da ke kewaye da yankin.

Al'amarin ya faru ne a wasu yankunan karamar hukumar Lau, da Katibu da kuma sauran kauyukan da ke kewaye da yankin.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, "Wasu mutane ne da ake zargin Fulani ne suka kai harin da yin harbe-harbe da kuma cinna wa gidajen jama'a wuta".
"Yanzu haka muna da mutane 25 da aka kashe ban da wadanda suka gudu amma aka bi su a kan mashin aka harbe".
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar David Simal ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin.
Ya kuma kara da cewa, "An fara kai harin ne tun ranar Juma'a, kuma ko ranar Asabar ma mutum hudu ne suka rasu ranar Lahadi kuma mutane da dama ne suka mutu, amma kawo yanzu ba za mu iya tabbatar da adadinsu ba".
"An samu mutanen da suka jikkata kuma tuni aka garzaya da su asibi". In ji kakakin rundunar.
Zaman dar-dar na sake karuwa a yankunan na jihar Taraba, sakamakon rikice-rikice da hare-hare da ake samu musamman a kwanakin baya-bayan nan