spon

Monday, September 3, 2018

RA'AYI: NA SAN DAI BA ZA A HANA ALLAH YI WA BUHARI HISABI BA

RA'AYI: NA SAN DAI BA ZA A HANA ALLAH YI WA BUHARI HISABI BA




RA'AYI:  Na San Dai Ba Za A Hana Allah Yi Wa Buhari Hisabi Ba

Daga Zee Taraba

Dan Allah masu yi wa Buhari makauniyar soyayya ida kun isa ku hana Allah ya yi masa hisabi ranar gobe tunda ku ba za ku fada masa gaskiya ba kuma ba za ku bari masu tsoron Allah su fada masa gaskiya ba.

Mun lura abun naku ya soma wuce gona da iri, har ta kai ga kuna zagin Malaman addini akan siyasar banza wadda kwata-kwata duk rantsi duk jimawa shekaru takwas kacal ake akan kujerar.

Mulkin Buhari babu hali Malami ya ce zai fito ya fadawa Buhari gaskiya sai a soma cewa wai malamin siyasa ne, idan kuma ya yaba Buhari sai a ce na addini ne tsabar son zuciya irin namu.

Wai shi Buhari yafi karfi a fada masa gaskiya ne?

A ce wai Malaman addini a ringa zagin su akan wani dan Siyasa wanda kullum shi a yabon kansa yake shi kadai tsabar son rai?

To bara ku ji na fada muku, idan kun hana a fada masa gaskiya a nan gidan duniya, to ku sani baku isa ku hana Allah ya yi masa hissabi ba bisa ga yadda ya gudanar da mulkinsa da kuma rayuwarsa ba ranar gobe.

Saboda haka a yi hattara dan Allah, Siyasa ba hauka bane.

ANA TARO AKAN RAYUWAR MARIGAYI MAMMAN SHATA A FAGEN WAKA

A Najeriya a yau ake fara wani taron masana a kan rayuwar marigayi Dr Mamman Shata da basirarsa a fagen waka.
Masana daga kasashen duniya ne za su gabatar da makala a wajen taron, wanda Cibiyar nazarin harsunan Najeriya ta shirya, tare da hadin gwiwa da Sashen Nazarin harsunan Najeriya da kuma sashen Nazarin kimiyyar harshe na jami`ar Bayero ta Kano.
Taron dai yazo ne a daidai lokacin da wasu ma`abota tsofaffin wakoki irin na shata da dangoginsa ke kukan cewa kafafen yada labarai na mai da su saniyar-ware a filayen shakatawa da suke gabatarwa a cikin shirye-shiryensu.
Wannan na faruwa ne, kasancewar hankalinsu ya fi komawa kan mawakan nanaye, suna fargabar cewa irin hkima da azancin da ke cikin tsofaffin wakokin ka iya bacewa idan aka ci gaba da tafiya haka.

Ronaldo, Modric, Salah unveiled in FIFA shortlist for World Player of the Year trophy. Messi fails to make the cut off

Ronaldo, Modric, Salah unveiled in FIFA shortlist for World Player of the Year trophy. Messi fails to make the cut off
Cristiano Ronaldo is locked in a race to be crowned FIFA men’s world player, alongside  former Real Madrid teammate Luka Modric and Egypt’s Mohamed Salah.

Sunday, September 2, 2018

FIM DIN ‘IN SEARCH OF THE KING’ YA SAMU GOYON BAYAN MASARAUTAR RINGIM

FIM DIN ‘IN SEARCH OF THE KING’ YA SAMU GOYON BAYAN MASARAUTAR RINGIM.

AUTHOR/AREWAINFINIT



A farkon watan nan na Yuli aka shiga aikin wani fim na turanci mai suna In Serach of the King, wanda yake ba da tarihi da yanayin masarautar Kasar Hausa tun tsawon shekaru masu yawa da suka gabata. Duk da cewar  fim ne da aka yi shi da harshen turanci amma idan ka dauke yaren na turanci da aka yi amfani da shi, to duk wani abu da aka nuna a fim din yana nuna ydda tsarin rayuwar masarautar kasar Hausa take ta fannin al’adu, ilimi, mulki da mu’amalarsu ta yau da gobe. Wani abin birgewa game da wannan fim din kusan za a iya cewa shi ne fim na farko da aka nuna yadda Sarautar kasar Hausa take a zahiri, ba wai kwaikwayo ba. Domin kuwa an yi amfani da gadon sarautar Ringim ne inda Sarkin na Ringim dake jihar JIgawa ya amince a yi aikin fim din a masarautarsa kuma ya bayar da aron duk wata fada da ake bukata domin gudanar da ikin fim din.  Kuma ya ba da mutanesa da suka rinka kula da aikin don su tabbatar an bi tsarin sarautar ba tare da an yi mata kutse ba, kamar yadda aka saba yi a sauran finafinan da ake yi a Kannywood. Fim din dai labarin masarautu ne masu karfi har guda uku a kasar Hausa kuma Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Abba Almustapha suka fito a matsayin sarakuna. Sai Nafisa Abdullahi da ta fito a matsayin Gombiya kuma jarumi mai tasowa Abdullah Amdaz ya fito a matsayin Yarima. Kabiru Musa Jammaje shi ne ya dauki nauyin shiryawa. Ganin yadda fim din ya samu amincewa ga masauratar Ringim har aka yi aikin a cikin fadar, mun tambayi jagoran shirin Malam Kabiru Jammaje a game da matakan da suka bi har suka samu amincewar masarautar da kuma yadda aikin ya gudana. Inda ya shaida mana cewar, “Tun da farko ma dai da muke yin aiki a kan rubuta labarin, gaskiya ba mu dauka za mu je  har Ringim domin yin aikin ba, saboda a tunaninmu za mu samu wajen da za mu yi aikin a kusa, sai ya zama mun je gurare da dama amma sai muka ga bai yi mana yadda muke so ba, don haka sai aka kawo shawarar a tafi wajen Sarki Ringim za a iya samu. Don haka da muka je muka yi gaisuwa kuma sai muka ba da takardar neman izini ta a ba mu dama mu yi amfani fa masarautar don gudanar da aikin, kuma abin farin ciki suka nuna goyon baya suka aiko mana da takardar amincewa ta hannun Danmajen Ringim. Kuma wani abu a ya zo mana bazata wanda ya kara inganta mana aikin shi ne yadda masarautar ta ba mu mai kula da mu ya kasance tare da mu wato Yariman Ringim. Don sun ce suna kallon finafinai da ake yi na sarauta, amma ba a nuna masarautu yadda ya kamata, don haka tun da a masarautarsu za a yi ba za su zuba ido su ga an murguda yadda tsarin masarauta yake ba, don haka ba biyan su muka yi ba sune suka ga dacewar yin hakan, don suna daukar cewar wani nauyi ne a kansu musamman da muka nuna musu cewa fim din za a yi shi da turanci ne kuma zai shiga kasashen Turai da ma wasu nahiyoyi na duniya, don haka suka ga hakkinsu ne su tsaya su tabbatar an yi tsarin sarautar da ta shafi Arewacin Najeriya yadda ya kamata. Kuma na gamsu sosai da tsayawar tasu domin kuwa da an bar mu da kanmu da mun yi kurakurai. Saboda hatta yadda Sarki yake zama da kafar da zai kada da yanayin yadda yake magana da saka kaya duk sai da suka nuna mana don ko rawani ma sune suka daura wa Sarki da Galadima da Waziri da Shamaki, don kowa da yanayin yadda yake rawaninsa. Don shi da kansa Yariman wato dan Sarkin ya ce fim din duk wanda ya kalle shi in dai ya san tsarin sarautar to ya san an bi tsarin yadda ake gudanar da ita. Don sarauta aka nuna ta sosai ba ta wasan kwaikwayo ba, kuma gaskiya an samu canji sosai. Ya ci gaba da cewa, “Duk fim din ya kunshi masarautu ne guda uku masarautar Tumashe wadda Sarkinta shi ne Abba Almustapha, sai masarautar Gwani da wadda Yakubu Muhammad ne Sarki sai masarautar Salbana da Alinu Nuhu ya zamo Sarki. Kuma a yanzu  mun  fara ne da masarautar  Salbana a garin Ringim, yanzu abin da ya rage mana sune sauran masaautu guda biyu ta Gwarida da kuma ta Kumashe. Saidai su ba a garin Ringum din za a yu su ba, za a yi su ne a garin Kano da kuma Danbatta.”
Sai dai ganin yadda Masarautar Salbana ta samu kulawa daga masarautar Ringim, kasancewar sauran masarautun ba a can za a yi su ba, ko su ma za su samu kulawa daga masarautar? Sai Jammaje ya ce, “Lallai mun yi magana da Yariman kuma ya tabbatar mana cewar duk da ba a garinsu ba ne zai zo da kansa a yi komai a gabansa. Don haka muna godiya a gare shi da kuma masarautar Ringim bisa gudunmawar da suka ba mu.”

Shi ma Daraktan fim din Balarabe Murtala Baharu ya shaida mana cewar, “Ni abin da zance na amfana da shi a fim din In Search of the King duk fim na duniya idan za a yi ana karuwa da Darakta ne daga irin yadda yake gudanar da aikinsa, amma a wannan fim din ni na kara ilimi saboda irin abin da aka zo da shi na nuna ka’idar yadda sarauta take zaman fada, mu’amala, maganganu, sanya tufafi da yadda ake zama. Ni a rayuwata ban taba tunanin haka fada ake ba, don haka a matsayina na mai ba da umarni na karu sosai kuma  kalubalen da na fuskanta ban taba yin aiki ina tare da masu ba da umarni har guda hudu ba sai a In Search of the King. Wanda yake  kula kalmomin da ake firtawa daban, wanda yake kula da kayan da ake sakawa daban, wanda yake lura da  zaman da ake yi daban. Sannan wadanda suke kula da aikin da ni kaina nake yi daban. Don haka wannan fim din ya zama zakaran gwajin dafi. Kuma abin da ya fi saka ni farin ciki da shi mai fim din ya ce shi a shirye yake da ya sake linka wani kudin da ya yi wa fim din kasafi domin a samu aiki mai inganci don bin diddigin da ake yi wa  fim cin bai sa shi ya karaya ba, kuma ya yarda fim din da aka ce za a yi sati biyu, ya amince ya kai sati 4 ma ana yin aikinsa. Don haka wannan ba karamar nasara ba ce. Kuma daman abin da muka rasa a cikin finafinanmu kenan shi ya sa za ka ga ana samun kurakurai, domin ka ga a cikin wannan aikin namu akwai rana guda  da ta zamo sin daya kawai muka dauka saboda bin tsari na ya kamata a dauke shi daidai yadda mai kallo zai dauke shi ya kalle shi a matsayin gaske ne ake yi shi ba wasa ba.” Nafisa Abdullahi ita ce jarumar da ta fito a matsayin  Gimbiya a fim din, ta bayyana cewa, “Duk da cewar wannan fim din ba shi ne na farko da nake fitowa a cikin sarauta ba, to shi wannan ya zo mini da siffa ta daban, kasancewar sa na Turanci. Don haka a nan zan iya cewa In Search of the King ya bambanta da sauran finafinan da na saba fitowa, kuma aikin ya burge ni sosai don na ji dadinsa.” Shi ma jarumin fim din Abdullahi Amdaz wanda ya kasance fim din ne na farko a gare shi da ya zamo babban jarumi, ya shaida mana cewar, “Na yi farin cikin kasancewa a matsayin jarumin wannan fim din, “Duk da cewa shi ne fim na farko da na zamo babban jarumi a cikinsa. Don haka sai na ji a zuciyata zan yi kokari na yi duk wani abu da zai ba da fa’ida kuma ya fito da kima da darajar aikin. Na fito a matsayin Bello da ya ke yawo a tsakanin masarautu guda uku domin neman cimma wani burina kuma a hakan na samu kaina a yanayi kala-kala don na samu na yi.” Zuwa yanzu dai an kammala kashin farko cikin kashi uku na fim din har an tafi hutu, sai a watan Oktoba za a ci gaba da kashi na biyar da na uku a garin Kano da kuma Danbatta. Fim din dai ya kunshi jarumai masu yawan gaske da suke aiki a cikin fitattun ‘yan Kannywood akwai Ali Nuhu, Abba Almustapha, Yakubu Muhammad, Nafisa Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Rukayya Dawayya, Shehu Hassan Kano, Shu’aibu Yawale, Tijjani Faraga da sauransu.

YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
 TITTLE YACCE AKE HADA KOSAI NA KIFI.
KAYAN HADI*
  • Kwai
  • Kifi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Fulawa
  • Maggi
  • Gishiri
  • Man gyada
 
*YADDA ZA KIYI*
Da farko ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki ďora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cicire 'kayar shi sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, ki fasa 'kwai kaďan ki zuba a ciki, ki ďauko fulawa ki zuba(hikimar sa fulawa dan ya haďe jiki ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe
 
SPINACH EGG SAUCE

INGREDIENTS:
1. Spinach (Alayyaho)
2. Eggs, oil
3. Tattasai, tarugu, albasa and garlic.
 
PROCEDURE: A wanke alayyaho a yayyanka qanana, sai a yayyanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko zaki samu tukunyar da babu komai a wuta ki juye alayyahon duka ki ďan turara sa. In kina da steamer zaki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.
Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in ya ďan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu ki juye alayyahon ki jujjuya su hade.
Ki kaďa eggs ki juye a ciki ki juya su haďe da kyau, in ya gama soyuwa sai ki sauke. Zaki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma doya da dankali.
Note: Zaki iya zuba isashen kwai ni nafi son shi a haka. Ba dole sai spinach ba zaki iya yi da sauran ganyayyaki. Kuma zaki iya yi babu kayan miya, idan kika yi steaming alayyahon tare da albasa sai ki kaďa kwai ki juye a ciki. A kula sosai idan kin yanka alayyaho ne kafin ki yanka to ki zuba ruwa isashe yanda zai taso sama sai ki kwashe zaki ga qasan ya koma qasa in ba haka ba zaki rinqa ci kina jin qasa. Yana da dadi in aka sanya a shinkafa. Ga kuma qara lfy.
 
Gashashen Kifi/ Grilled Fish
Kayan Hadi:
1. Kiyin Karfasa / Tilapia
2. Albasa, lemun Tsami, Citta, Kanunfari, Masoro, Tafarnuwa, Garin Yaji ko Tarugu.
3. Maggin Knorr, Gishiri, Kori, Thyme, da kayan Qamshi da Dandano
4. Myan Gyada.
Yadda Zaki Sarrafa: Ki wanke kifin ki ciki da bai, saka hannu har cikin bakin kifin ki wanke shi sosai. Bayan kin wanke sai ki tsane ruwan in sauri kike yi kisa towel ko tissue ki cire ruwan.
Daga nan sai ki daka ko kiyi blending kanunfari da masoro, citta, thyme, da sauran su. In kuma kina da garin su shikenan. Sai ki juye a mixing bowl.
Sannan ki dauko albasa kamar rabi haka ki saka, ki zuba tafarnuwa biyu manya, idan ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi blending ko daka yayi luqui luqui. Haka nan in tarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi.
Daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba curry kadan, ki zuba knorr da gishiri, sannan ki matse lemun tsami qaramin cokali daya ki zuba. Sai ki zuba oil yanda hadin zai kama jikin kifin.
Bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki. Sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a fridge yayi kamar minti 30 in a freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi qanqara ba.
Daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da oven ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin ki, kina yi kina jujjuya wa har ya gazu.
Hadin Sauce/Sauce
Kayan Hadi:
1. Albasa biyu ko uku
2. Tarugu, Tattasai da Green pepper
3. Tafarnuwa 1
4. Gishiri da Maggi knorr
Yadda Zaki Hada Sauce: Farko zaki yanka albasanki da tattasai da green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura mai a tukunya kamar quater qaramin ludayi, in yayi zafi ki zuba albasan da tattasan, ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba niqaqqen tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa tare da sinadarai, sai ki dan zuba ruwa kadan yanda zasu dahu. Zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida.
Daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din a sama. Ai haka zaki ji kawai yana shigewa cikin tumbin maigida yana santi.
Kada a manta a ajiye wa mai gida lemun tsami na wanke hannu bayan ya gama ci saboda qarni. Sannan a tabbata an saka ginger ko citta, tafarnuwa da kanunfari don suna da muhimmanci a gashi.

YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

HOME/FOOD MAKING
AUTHOR/AREWAINFINIT
      TITTLE:YACCE AKE KUNUN SEMOVITA

Abubuwan hadawa

  • Semonvita kofi 1/2
  • Madara cokali 6
  • Suga dai dai dan dano

Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tukunyarki, ki sa ruwa ki dora a wuta ya tafasa.
  2. Sai ki dauko semonki ki dama da ruwa ya yi kamar za kiyi talge.
  3. Sai ki duba idan ya tafasa sai ki zuba a kan ruwan ki juyashi sosai.
  4. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba a kwano ki sa madara da suga sai ki juya ki zubawa kowa a kofi.

A sha dadi lafiya. Na gode sai mun hadu girki n a gaba.

Ba na tsoron fafatawa a zabe na gaskiya — Buhari

HOME/POST FILE UNDER LABARAI
AUTHOR:AREWAINFINIT
DATE:SUN SEP 2 2018
 
NIGERIA PRESIDENCY
Image captionGwamnan jihar Lagos, wanda ake rade-radin cewa zai fice daga APC, na cikin tawagar Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba ya tsoron fafatawa a zabe idan za a gudanar da shi cikin gaskiya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar China a birnin Beijing inda yake ziyara.
A cewar sa, "Ba na jin tsoron karawa a zaben da za a gudanar cikin gaskiya saboda shi ne ya sa na zama shugaban kasa. Na san irin faman da na yi inda sau uku ina tsayawa takara ina faduwa zabe amma ina kalubalantar sakamakon sa a kotun koli."
"Da na fadi a zabe karo na uku na ce 'Allah ya saka min'; daga bisani aka yi amfani da fasahar na'ura wuririn gudanar da zabe kuma hakan ya taimaka mana,' in ji Shugaba Buhari.